Hukumar leken asiri ta tura sako ga lauyan Zakzaky kan batun hanashi fita waje

Hukumar leken asiri ta tura sako ga lauyan Zakzaky kan batun hanashi fita waje

  • Hukumar leken asiri ta Najeriya ta bayyana matsayar ta kan zargin tana rike da fasfo na Malam Zakzaky
  • Hukumar ta bayyana haka ne bayan da IMN ta zargi gwamnatin Najeriya da hana malamin fita nemo magani a kasar waje
  • Hukumar ta fayyace batu, ta kuma tura wasika ga babban lauya Femi Falana kan batun mai muhimmanci

Abuja - Hukumar Leken Asiri ta Najeriya (NIA) ta shaidawa kungiyar Harkar Musulunci ta Najeriya (IMN) cewa ba ta karbi fasfo na kasa da kasa na shugabanta, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, da matarsa, Zeenah ba.

Hukumar NIA ta yi wannan karin haske ne yayin zanga-zangar da kungiyar ta IMN da lauyan kare hakkin dan adam, Femi Falana (SAN), suka yi kan kin amincewa da gwamnati ta yi na sakin takardun su Zakzaky.

Ma’auratan ba za su samu damar cillawa kasar waje neman magani ba bayan da babban kotun jihar Kaduna ta sallame su tare da wanke su.

Hukumar leken asiri ta tura sako ga lauyan Zakzaky kan batun hanashi fita waje
Sheikh Ibrahim Zakzaky | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Amsa mai tsauri daga NIA tare da Lambar N/OPS/14’4A/VOL.2, mai kwanan wata 12 ga watan Agusta da sa hannun wani mai suna I. Giwa a madadin Darakta Janar na NIA, Ahmed Rufa’i Abubakar, an aika shi zuwa ga babban lauya Falana.

An mayar da martanin mai taken, 'Re: Bukatar a saki fasfo na kasa da kasa (da sauran takardu) na Sheikh Ibrahim Yaqub El-Zakzaky da Malama Zeenah Ibrahim', wanda jaridar The Punch ta ce ta samu a ranar Lahadi 22 ga watan Agusta.

Wani yankin wasikar ya ce:

“An umarce ni da in shaida karbar wasikar ku mai kwanan wata 2 ga Agusta, 2021, kan batun da ke sama kuma in sanar da ku cewa hukumar ba ta rike da fasfo ko wasu takardu mallakin Sheikh Ibrahim Yaqub El-Zakzaky da matarsa, Malama Zeenah Ibrahim."

An ruwaito cewa Sakataren IMN, Abdullahi Muhammad, ya tura koke ga manyan kungiyoyin duniya kan cewa, Gwamnatin Najeriya ta bi umurnin kotu kuma ta saki fasfo din El-Zakzaky da matarsa.

Yadda Kotu ta wanke Sheikh Zakzaky da matarsa, ta umarci a sake su

Rahotanni da muke samu sun bayyana cewa, a yau 28 ga watan Yuli, an yanke hukunci kan Zakzaky da matarsa, inda tuni aka wanke su daga zargi.

A cewar lauyan Zakzaky, Barista Sadau Garba, kotun ta wanke waɗanda ake zargin daga zargi takwas da gwamnatin Jihar Kaduna ta gabatar mata.

Rahoton ya ce tuni bayan yanke hukuncin aka zarce da Zakzaky zuwa gida nan take, kuma ba a tsaya sauraran 'yan jarida ba.

Tun farko, ba a 'yan jarida da sauran jama'a damar shiga zauren kotun ba.

A cewar rahotanni, mai shari'a Gideon Kurada ne ya jagoranci shair'ar cikin sirri.

A cewar gidan talabijin na Channels, zaman sauraran shari'ar ya shafe akalla sa'o'i takwas kafin cimma wanke malamin da matarsa, tare da ba da umarnin sakinsu.

An dage shari'ar Abduljabbar zuwa wasu makwanni masu zuwa

A wani labarin daban, an dage shari'ar Abduljabbar zuwa wasu makwanni masu zuwa Lauyar gwamnati ta bayyana dalilan da yasa ta roki a dage shariar zuwa wani lokaci in da take cewa:

"Mun saurari jawabansa, kuma bayanansa azarbabi ne.

Mun nemi kotu ta dage shari'ar ne domin mu kawo tuhumar da muke yi masa.

"Ai caji ya kunshi dukkan wani bayani da muke bukata. Lauyan wanda ake kara ba shi ne zai fada mana yadda za mu tsara kararmu ba. Kuma muna rokon kotu ta ba mu 25 ga watan Agusta, 2021, domin a ci gaba da shari'a."

Bayan doguwar caccaka tsinke, Alkali ya gamsu da bayanai daga dukkan bagarori, ya kuma yanke hukunci, inda ya amince da dage shari'ar zuwa wani lokaci.

BBC ta ruwaito cewa, Alkali ya dage shari'ar har zuwa nan da makwanni uku, wato za a sake zama ranar 18 ga watan Agustan wannan shekara. Hakazalika, malamin zai ci gaba da zama a gidan gyaran hali. Dukkan bangarori sun gamsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel