Sai mun kakkabo ragowar 'yan ta'addan dake yankin tafkin Chadi, MNJTF

Sai mun kakkabo ragowar 'yan ta'addan dake yankin tafkin Chadi, MNJTF

  • Manjo janar Abdul-Khalifah Ibrahim, kwamandan MNJTF, ya bukaci rundunar soji da tayi shirin karasa ragargaje sauran mayakan Boko Haram dake wuraren tafkin Chadi
  • Shugaban fannin yada labarai na sojojin, Kanal Muhammad Dole ya bayyana hakan a wata takardar ranar Juma’a inda yace Ibrahim ya fadi hakan ne a wani zagaye da suka yi
  • Dole yace a makon da ya gabata kwamandan ya kai ziyara Bangare na 3 na MNJTF dake monguno a Najeriya, bangare na daya dake Moura a Kamaru da bangare na biyu dake Bagasola a Chadi

Yankin Tafkin Chadi - Manjo janar Abdul-Khalifah Ibrahim, kwamandan sojojin MNJTF ya bukaci rundunonin soji da su shirya ragargazar ragowar mayakan Boko Haram da suke wuraren tafkin Chadi.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, a wata takarda ta ranar Juma’a, Shugaban fannin yada labaran soji na MNJTF, Kanal Muhammad Dole ya ce Ibrahim yayi wannan maganar ne a lokacin da ya zagaya sansanonin sojojin yankin.

Kara karanta wannan

Olusegun Obasanjo yayi magana akan ta’addancin da ke ta'azzara a Najeriya

Sai mun kakkabo ragowar 'yan ta'addan dake yankin tafkin Chadi, MNJTF
Sai mun kakkabo ragowar 'yan ta'addan dake yankin tafkin Chadi, MNJTF. Hoto daga Dailynigerian.com
Asali: UGC

Dole ya ce a makon da ya gabata kwamandan ya kai ziyara bangare na uku dake Monguno a Najeriya, bangare na daya dake Moura a Kamaru da bangare na boyu dake Bagasola a Chadi.

Ya ce kwamandan ya sanar da rundunar sojin cewa su sabunta niyyarsu na yakar makiya don a yi gaggawar kawo karshen wannan yakin, Daily Nigerian ta ruwaito hakan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa, Ibrahim ya yabawa sojoji da mazaje akan kwarin guiwarsu, dagiya da tsayawa akan aikinsu wanda ya janyo ‘yan ta’addan suka rage yawa.

Kwamandan ya mika ta’aziyyarsa ga sojojin da suka mutu kuma ya yi fatan su samu rahama.
Ya yi kira akan sabunta niyya da kuma dagewa wurin mayar da hankali akan tsarin MNJTF don samun nasara.
Ya ce ya saurari duk matsalolin da ake fuskanta kamar yadda kwamandoji suka bayyana masa kuma zasu zauna su duba lamarin.

Kara karanta wannan

2023: Cancanta ya kamata a bi wajen zabar wanda zai zama Shugaban Najeriya, in ji Yahaya Bello

Ya yabawa rundunonin akan kokarin da suke yi wa Najeriya, Nijar, Kamaru, Chadi da jamhuriyar Benin akan yadda suka yarda da MNJTF da kuma yin yadda ya dace. Ya yi godiya ga LCBC, AU da EU akan taimakon da suke yi wa MNJTF.

EFCC ta sako tsohon gwamna bayan damke shi da tayi da sa'o'i

An sako tsohon gwmanan jihar Abia, Sanata Theodore Orji bayan kwashe wasu sa’o’i a ofishin EFCC.

Gidan talabijin din Channels sun ruwaito yadda jami’an hukumar EFCC sun damki sanatan a filin jirgin Nnamdi Azikwe dake Abuja a ranar Alhamis, 19 ga watan Augusta.

Hukumar EFCC ta sako tsohon gwamnan bayan ya sha tambayoyi a kan harkokin kudaden da yayi tsakanin 2007 da 2015 inda ake zargin rashawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel