Dalilin da ya sa nake kunyar kasancewa dan APC, tsohon Shugaban majalisar dattawa ya magantu

Dalilin da ya sa nake kunyar kasancewa dan APC, tsohon Shugaban majalisar dattawa ya magantu

  • Ken Nnamani, tsohon shugaban majalisar dattijai, ya yi kira da a sake fasalin jam’iyyar All Progressive Congress reshen Enugu
  • Dan siyasar ya ce ya kamata membobin jam'iyyar su himmatu wajen kara yawan magoya bayan APC a jihar
  • Nnamani ya bayyana cewa mutanen da suka cancanta ne kawai ya kamata a ba damar jagorantar jam'iyyar reshen Enugu

Jihar Enugu - Wani tsohon shugaban majalisar dattijai, Ken Nnamani, ya koka kan yadda jam'iyyar All Progressive Congress (APC) ta kasa cin zabe a jihar Enugu.

Ya ce yana jin kunyar kasancewa a jam'iyyar da ba ta cin zabe a jihar.

Dalilin da ya sa nake kunyar kasancewa dan APC, tsohon Shugaban majalisar dattawa ya magantu
Ya ce akwai bukatar sauya jam'iyyar reshen jihar
Asali: Facebook

Kamar yadda The Cable ta ruwaito, Nnamani ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, 21 ga watan Agusta a Enugu yayin zaman kwamitin daukaka kara na APC.

Kara karanta wannan

APC, FG sun gazawa 'yan Najeriya - Jigon Jam'iyyar ya magantu, ya yi hasashe mara kyau kan 2023

Ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Jam'iyyar tana habbaka a jihar amma nasararta ta dogara ne da cin zabe. Mutane sun tsorata da shugabannin.
“Ina jin kunyar kasancewa cikin jam'iyyar da ba ta cin zabe. Wannan shine dalilin da ya sa muke son sake canza jam'iyyar don kawo shugabannin da ba za su yi amfani da ita don kasuwanci ba.''

PM News ta ruwaito cewa ya ce gazawar da jam'iyyar APC reshen jihar Enugu ta yi a cikin shekaru bakwai da suka gabata ya sanya ya zama dole a sauya jam'iyyar.

Dan siyasar ya soki 'yan jam'iyyar da ke yin kalaman batanci ga APC a kafafen yada labarai.

Ya kuma soki wasu tsaffin shugabannin jam'iyyar a jihar kan rantsar da mambobin zartarwa na gundumomi kwana biyu bayan babban taron.

Nnamani ya ce kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar bai ba da izinin kowane babi ya rantsar da kowa ba.

Kara karanta wannan

2023: Yemi Osinbajo ya bayyana abin da zai faru da APC bayan Shugaba Buhari ya bar mulki

A cewarsa, an yi rantsuwar ne ba bisa ka'ida ba.

A wani labarin, wasu fusatattun ‘yan jam’iyyar APC kimanin mutum 100, sun shigar da karar shugabanninsu a kotu a ranar 19 ga watan Agusta, 2021.

Daily Trust ta ce wadannan mutanen suna karar shugaban kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar APC, gwamnan jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni.

A wannan kara da ‘ya ‘yan na APC suka shigar a kotu, sun hada da Ministan shari’a, kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami SAN.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel