An yi karar Shugaban APC, Mala Buni, ana so Kotu ta tsige daukacin shugabannin rikon kwarya

An yi karar Shugaban APC, Mala Buni, ana so Kotu ta tsige daukacin shugabannin rikon kwarya

  • Wasu suna karar Shugabannin jam’iyyar APC a Kotun Tarayya da ke Abuja
  • ‘Ya ‘yan jam’iyyar na reshen Benuwai suna so a rusa kwamitin rikon kwarya
  • Lauyan da ya shigar da kara yace AGF bai da ikon nada wa APC shugabanta

Benue - Wasu fusatattun ‘yan jam’iyyar APC kimanin mutum 100, sun shigar da karar shugabanninsu a kotu a ranar 19 ga watan Agusta, 2021.

AGF, Buni, INEC za su kare kansu

Daily Trust ta ce wadannan mutanen suna karar shugaban kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar APC, gwamnan jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni.

A wannan kara da ‘ya ‘yan na APC suka shigar a kotu, sun hada da Ministan shari’a, kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami SAN.

Kara karanta wannan

Bayan ya koma APC, ‘Ya ‘yan Jam’iyya sun fara rigima da Yakubu Dogara a jihar Bauchi

Rahoton yace haka zalika masu karar sun sa hukumar INEC mai gudanar da zabe na kasa da kuma wasu a cikin wadanda za su kare kansu a gaban kotu.

Wadanda suka shigar da wannan kara a babban kotun tarayya da ke zama a Abuja, wasu daga cikin ‘ya ‘yan jam’iyyar APC ne na rashen jihar Benuwai.

Abin da Lauya yake cewa

‘Ya ‘yan jam’iyyar wadanda suke ganin ba a yi masu daidai a APC sun dauki hayar Samuel Irabor a matsayin lauyan da ya shigar masu da kara gaban Alkali.

Shugaban APC, Mala Buni
Mai Mala Buni da Bola Tinubu Hoto: www.naijanews.com
Asali: UGC

Samuel Irabor ya roki Alkali ya ruguza kwamitin mutum 13 da majalisar koli ta NEC ta kafa a matsayin shugabannin rikon-kwarya na jam’iyyar APC.

Irabor ya na ikirarin cewa Abubakar Malami bai da hurumi a doka da zai rantsar da gwamnan Yobe, Mai Mala Buni a matsayin shugaban rikon kwarya.

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Rikicin cikin gidan da ya ke damalmala Jam’iyyar APC ya kara cabewa

A cewar masu wannan kara, a dokar APC ta shekarar 2014 wanda aka yi wa garambuwal, Ministan shari’ar bai cikin majalisar NEC ko NWC na jam’iyyar.

Da wannan ne ‘ya ‘yan jam’iyyar suka kafa hujja, suke neman a sauke shugabannin wucin-gadin.

Ana fama da rigingimu a APC

A gefe guda, ku na da labarin ‘Dan Majalisar Kano, Sha'aban Ibrahim Sharada, ya soki zabukan shugabannin mazabu da Jam’iyyar APC ta gudanar kwanaki.

A dalilin irin haka ne shugaban rikon kwarya na kasa, Mai Mala Buni ya nada kwamitin da zai yi sulhu a jihohi, amma rikicin APC ya ki kare wa a jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel