Borno: An kama Malam Ayu da ya amshe miliyoyi hannun wani da sunan zai mayar da shi attajiri cikin sati biyu

Borno: An kama Malam Ayu da ya amshe miliyoyi hannun wani da sunan zai mayar da shi attajiri cikin sati biyu

  • Jami'an hukumar EFCC sun kama wasu mutane biyu kan batun yin asirin samun dukiya a Borno
  • Wani Abubakar Bakura ya ce wani Malam Ayu Sugum ne ya ce ya kawo N2.9 ya yi masa asirin yin arziki cikin sati biyu
  • Malam Ayu ya amsa cewa ya karbi kudi daga hannun Abubakar sannan ya bashi wani kyalle da magani na ruwa

Maiduguri, Jihar Borno - Jami'an hukumar yaki da rashawa na EFCC a Maiduguri jihar Borno sun kama mutane biyu kan zargin 'asirin samun kudi' a jihar Borno, The Cable ta ruwaito.

A cewar EFCC, daya daga cikin wadanda ake zargin, mai suna Malam Ayu Sugum, ya umurci wani Abubakar Bakura ya sato N2.9m daga wurin wanda ya ke yi wa aiki.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Atiku ya koka kan lamarin ta’addanci, ya ce lallai sai dai a sake fasalin kasar

Sugum, da aka gano cewa yana ikirarin cewa yana aiki da iskokai, ya yi wa Bakura alkawarin cewa zai yi masa asiri ta yadda zai zama attajiri cikin kwanaki 14, rahoton The Cable.

Borno: An kama Malam Ayu da ya amshe miliyoyi hannun wani da sunan zai mayar da shi attajiri cikin sati biyu
Borno: An kama Malam Ayu da ya amshe miliyoyi hannun wani da sunan zai mayar da shi attajiri cikin sati biyu. Hoto: The Cable
Asali: Facebook

Sanarwar ta EFCC ta fitar ya ce:

"Jami'an EFCC na Maiduguri sun kama wani mai ikirarin 'boka' ne, Mallam Ayu Sugum, kan zuga wani Abubakar Mustapha ya sato N2.9m (Naira Miliyan 2.9) daga wurin aikinsa da sunan za a masa asirin da zai zama attajiri."
"An kama shi ne a wani gida da ke Pompomari Bypass, Maiduguri, Jihar Borno bayan an ambaci sunansa yayin bincike kan korafin da wanda Bakura ke yi wa aiki ya shigar."

Abubakar ya amsa cewa ya sace N2.9m daga wurin mai gidansa ya bawa Ayu

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya jagoranci zaman FEC na farko, ya amince a sayo karnukan N650m

"Bayan kama shi a ranar 8 ga watan Yulin 2021, Bakura ya amsa cewa ya saci kudin mai gidansa. Ya kara da cewa Ayu Sugum ya amshe kudaden daga hannunsa, ya masa alkawarin zai azurta shi cikin makonni biyu.
"Abubakar ya yi ikirarin an bashi wani ruwan magani da kyalle kuma duk lokacin da ya sha maganin ya kan gusar masa da hankali ya manta abubuwa da suka faru tsawon kwanaki kuma daga bisani ya sato kudin ya bawa 'bokan'."

Abinda Malam Ayu ya ce?

"Da aka masa tambayoyi, Sugum ya amsa cewa ya bawa Abubakar kyalle da wani ruwan magani ya sha, amma ya yi ikirarin kudin da ya karba hannunsa bai kai N2.9m ba."

EFCC ta kara da cewa za a gurfanar da mutanen biyu a kotu idan an kammala bincike.

'Yan sanda sun damke ma'aikacin banki da ya kwashewa kwastoma N10m daga asusunsa

A wani labarin daban, Hukumar ‘yan sandan jihar Oyo sun kama wani Adeyemi Tosin, mai shekaru 36, wanda ma’aikacin banki ne bisa zarginsa da kwasar naira miliyan 10 daga asusun wani abokin huldar bankin, Oladele Adida Quadri.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Jami'an Yan Sanda Na Musamman Sun Ceto Karin Mutum 33 Daga Cikin Musulman da Aka Kaiwa Hari a Jos

Kakakin hukumar, DSP Adewale Osifeso, ya bayyana hakan a wata takarda a ranar Talata, 17 ga watan Augusta, inda yace Tosin ya saci kudin Quadri, mai shekaru 78 ne da sunan zai taimake shi a reshen bankin na Ibadan bisa matsalar da ya samu wurin cirar kudi a ranar 12 zuwa ranar 13 ga watan Augusta.

Binciken ‘yan sandan ya haifi da mai ido sakamakon umarnin kwamishinan ‘yansandan jihar, Ngozi Onadeko, wacce tasa a yi bincike na musamman.

Asali: Legit.ng

Online view pixel