Abokan Ango Yusuf Buhari sun yiwa direban da ya tuka su kyautar N500,000

Abokan Ango Yusuf Buhari sun yiwa direban da ya tuka su kyautar N500,000

  • Abokan ango Yusuf Buhari, 'dan shugaba Buhari sun baiwa direbansu babban kyauta
  • A bidiyon da ya bazu yanzu, abokan angon day baya daya suka hada masa kudi
  • Abokan ango na kan hanyarsu ta zuwa wajen liyafar cin abincin dare

Kano - Abokan angon 'dan shugaba Muhammadu Buhari, Yusuf, wanda ya angwance ranar Juma'a sun yiwa direban da ya kaisu ihsani mai ban mamaki.

Yusuf, wanda shine dan shugaba Buhari daya tilo ya auri diyar Sarkin Bichi, Mai Martaba Nasir Ado Bayero, Zahra Bayero.

A bidiyon da @lindaikejiblog ta daura shafin Instagram, abokan angon sun baiwa direban mamaki inda suka hada masa sama da N500,000 nakadan.

Daya daga cikin abokan mai suna Osinbajo ya bada $100, yayinda wani kuma mai suna Yari ya bada N50,000, saura kuma sun bada nasu.

Bayan sun hada, sun mikawa direban kudin yana godiya.

Abokan Ango Yusuf Buhari sun yiwa direban da ya tuka su kyautar N500,000
Abokan Ango Yusuf Buhari sun yiwa direban da ya tuka su kyautar N500,000 Hoto: @lindaikejisblog
Asali: Instagram

An daura auren Yusuf Buhari da Zahra Bayero kan sadaki N500,000

Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Ibrahim Pantami, ne ya daura aure tsakanin 'dan Buhari, Yusuf Buhari, da diyar Sarkin Bichi, Zahra Bayero, a Masallacin kasar Bichi.

Yayinda babban attajiri, Alhaji Aminu Dantata, ya bada auren a madadin iyalan Sarkin Bichi; dan uwa kuma babban aminin Buhari, Malam Mamman Daura, ya karba aure matsayin wakilin ango kuma madadin shugaba Buhari.

Ga jerin wasu sannannu da suka halarci daurin aure:

1. Shugaba Muhammadu Buhari

2. Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo

3. Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan.

4. Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar

5. Tsohon shugaban kasan jamhurriyar Nijar, Mohammadou Issoufou

6. Alhaji Aminu Dantata

Shiga nan don ganin sauran

Kalli bidiyon:

Asali: Legit.ng

Online view pixel