Yanzu-yanzu: Tsohon gwamnan Oyo na mulkin soja, Tunji Olurin ya mutu
- Janar Tunji Olurin (mai ritaya) ya rasu bayan gajeriyar rashin lafiya a wani asibiti a Legas a cewar majiyoyin danginsa
- Tsohon janar din sojan ya kasance na kusa da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a jihar Ogun
- Olurin ya kuma kasance tsohon Shugaban Soja na jihar Ekiti tsakanin daga 8 ga watan Oktoba, 2006 zuwa 27 ga watan Afrilu, 2007
Tsohon gwamnan Jihar Oyo na mulkin soja, Janar Tunji Olurin (mai ritaya) wanda yayi shugabanci tsakanin 1985 da 1988 ya rasu, jaridar Vanguard ta ruwaito.
Olurin wanda ya kasance makusancin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya rasu a asibitin koyarwa na jami'ar jihar Legas (LUTH) a safiyar ranar Asabar, 21 ga watan Agusta.
Kamar yadda Jaridar Punch ta ruwaito, ya rasu yana da shekaru 77 a duniya.
Dan uwan mamacin, Funso Olurin, ne ya bayyana labarin a Abeokuta ranar Asabar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewarsa, Olurin ya mutu bayan gajeriyar rashin lafiya.
Olurin wanda ya kuma kasance tsohon Shugaban Soja na jihar Ekiti tsakanin 8 ga Oktoba, 2006 zuwa 27 ga Afrilu, 2007 ya fito daga Ilaro a yankin Ogun ta Yamma a jihar Ogun.
Ya kasance dan takarar Gwamna na Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a babban zaben 2011 a jihar Ogun.
A wani labari na daban, mun ji cewa akalla yan bindiga tara sun rasa rayukansu sakamakon rashin jituwa da ya auku tsakanin bangarorin tsagerun daban-daban a jihar Kaduna.
Gwamnatin jihar a ranar Juma'a ta bayyana cewa rahoton leken asiri da na jami'an tsaro sun tabbatar da hakan.
A cewar rahoton ChannelsTV, wannan rikici ya auku ne ranar Laraba a karamar hukumar Giwa ta jihar.
Asali: Legit.ng