Neman mafita: Secondus ya dira gidan Obasanjo yayin da rikicin PDP ya tsananta

Neman mafita: Secondus ya dira gidan Obasanjo yayin da rikicin PDP ya tsananta

  • Yanzu haka shugaban jam’iyyar PDP, Prince Uche Secondus yana Abeukuta, jihar Ogun, gidan tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo
  • Secondus ya isa katafaren gidan Obasanjon kuma ya nufi Olusegun Obasanjo Presidential Library a Oke Masan dake Abeokuta, tare da tawagarsa da misalin 12:19pm
  • Ko zama bai yi ba ya shiga taro don ana kyautata zaton yana fafutukar ganin ya makale a kujerarsa bayan ganin yadda rikici iri-iri suke ta ballewa a cikin jam’iyyar

Abeokuta, Ogun - Yanzu haka shugaban jam’iyyar PDP, Prince Uche Secondus yana gidan tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo dake Abeokuta jihar Ogun.

Daily Trust ta ruwaito cewa, shi da tawagarsa sun isa gidan Obasanjo inda suka mike dodar har OOPL da misalin karfe 12:19pm. Bai tsaya bata lokaci ba ya shiga ganin tsohon shugaban kasar.

Neman mafita: Secondus ya dira gidan Obasanjo yayin da rikicin PDP ya tsananta
Neman mafita: Secondus ya dira gidan Obasanjo yayin da rikicin PDP ya tsananta. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Shin mene ne dalilin ziyarar?

Wakilin Daily Trust ya tattaro bayanai akan yadda ake tunanin ziyarar da shugaban jam’iyyar ya kai bata wuce matsalolin da suke ta barkewa a cikin jami’iyyar ba.

Secondus yana iyakar kokarin ganin ya manne a kujerarsa iya wuya duk da rigingimun da suketa tasowa a jam’iyyar.

An samu rabuwar kawuna a Kwamitin ayyukan jam’iyyar PDP na kasa a makonni 2 da suka wuce inda wasu suka yi murabus kuma suka nemi Secondus da yayi murabus ya baiwa sabbi wuri.

Bayan an yi sulhu ne shugabannin jam’iyyar PDP suka amince da cewa za a sake zama don zaben sabon shugaban jam’iyyar a watan Oktoba.

Sai dai gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers, gwamna jiharsu Secondus ya nace akan lallai sai an canja shugaban jam’iyyar.

Duk da dai Obasanjo ya nuna cewa ya hakura da siyasar jam’iyya amma duk da haka yana da ruwa da tsaki a jam’iyyar PDP.

Dama Obasanjo ya taba cin zaben shugaban kasa har sau biyu a karkashin jam’iyyar PDP.

Luguden harbe-harben cikin dare yayi ajalin rayuka 5 a Cross River

Da daren Talata ne aka fara jin harbe-harbe ko ta ina a wasu unguwanni biyu dake wuraren Yala a jihar Cross River.

Anji harbin ne a O’oba da Okpame tun cikin dare har yanzu haka ba a daina ji ba kamar yadda wakilin Daily Trust na jihar yace.

Kwamishinan ‘yan sanda na Cross River ya tabbatar da tura jami’ansa da yayi yankin don kwantar da tarzoma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel