A hukunta tubabbun yan Boko Haram kawai, Kungiyar Arewa Consultative Forum ga FG

A hukunta tubabbun yan Boko Haram kawai, Kungiyar Arewa Consultative Forum ga FG

  • Kungiyar Arewa ta ce sama bata yarda a saki yan Boko Haram da suka mika wuya ba
  • A makon da ya gabata, kimanin yan Boko Haram 1500 sun ajiye makamansu
  • Gwamnatin Borno tace ita dai yanzu tana cikin tsaka mai wuya kan yadda zatayi da tubabbun yan ta'adda,

Kaduna - Kungiyar Arewa Consultative Forum, ta yi watsi da maganar yafewa yan ta'addan Boko Haram da suke mika wuya ga gwamnati da kuma sakinsu.

Shugaban kungiyar na kasa, Cif Audu Ogbeh, ya ce wajibi ne a hukunta yan ta'addan kan laifukan da suka aikata kan yan Najeriya.

Ogbeh, wanda tsohon Ministan noma ne, ya bayyana hakan a jawabin da ya rattafa hannu kuma kakakin kungiyar, Emmanuel Yawe, ya sake a Kaduna ranar Talata, rahoton ThePunch.

Yace:

"Muna ganin yadda yan ta'addan Boko Haram ke mka wuya da yawansu. cikinsu akwai masu hada bama-bamai, kwamandoji, masu fyade, da masu satan yara."

Kara karanta wannan

Nasara: Bidiyon 'yan ISWAP-Boko Haram na tururuwar tuba a Mafa dake Borno

"Saboda haka me zamuyi da su? Kawai mu sake su kuma mu yarda da su? Gaskiya da kamar wuya."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kungiyar tace idan har za'a saki wadannan mutan to a saki dukkan mutanen da aka tsare a gudan yari a fadin Najeriya gaba daya.

Yace:

"Muna taya gwamnan Borno, Shehun Borno, Sanata Ndume, da daukacin yan Najeriya wajen nazari kan wannan lamari kuma shawararmu itace: A hukuntasu ko kuma a saki dukkan wadanda ke tsare a fadin tarayya."

A hukunta tubabbun yan Boko Haram kawai, Kungiyar Arewa Consultative Forum ga FG
A hukunta tubabbun yan Boko Haram kawai, Kungiyar Arewa Consultative Forum ga FG Hoto: ACF
Asali: UGC

Gidan Soja: Dalilin da yasa muke karbar tuban mayakan Boko Haram da suka mika wuya

Rahotanni sun bayyana cewa Sojojin Najeriya sun yi bayanin cewa babbar yarjejeniya ta duniya wanda Najeriya ta sanya hannu a kansa bai yarda a kashe 'yan ta'adda da suka mika wuya ba.

Leadership ta ruwaito cewa kakakin rundunar, Brig-Gen Onyema Nwachukwu ne, ya bayyana haka a wata hira.

Kara karanta wannan

Kungiyar Kiristoci ta CAN ta fadi matsayarta kan kashe Muslulmai da aka yi a Jos

Ya sake nanata cewa sojojin da aka tura don “Operation Hadin Kai” sun karbi ‘yan ta’addan Boko Haram/ ISWAP da suka mika wuya bisa ga dokokin kasa da kasa da yarjejeniyar rikicin makamai.

An tattaro cewa sama da ‘yan ta’addan Boko Haram/ISWAP 3,000 ko dai aka kama su ko kuma suka mika wuya ga sojoji a arewa maso gabas a cikin watanni uku da suka gabata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel