Da dumi-dumi: Hukumar EFCC ta rufe wasu dukiyoyin tsohon gwamna Kwankwaso a Kano

Da dumi-dumi: Hukumar EFCC ta rufe wasu dukiyoyin tsohon gwamna Kwankwaso a Kano

  • Hukumar EFCC ta rufe wasu dukiyoyi mallakar Sanata Rabiu Kwankwaso a jihar Kano
  • An tattaro cewa matakin da hukumar ta dauka ya biyo bayan korafi da ta samu daga iyalan Ismaila Gwarzo, tsohon mai ba da shawara kan harkokin tsaro
  • Majiya ya nuna cewa Kwankwaso ya shiga lamarin ne saboda shi ya siya daya daga cikin kadarorin

Kano - Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta rufe wasu dukiyoyi mallakar Sanata Rabiu Kwankwaso a jihar Kano, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Tsohon gwamnan da ya mulki Kano sau biyu, Kwankwaso ya wakilci yankin Kano ta Tsakiya a zauren majalisar dokokin tarayya tsakanin 2011 zuwa 2015.

Da dumi-dumi: Hukumar EFCC ta rufe gidan tsohon gwamna Kwankwaso a Kano
Hukumar yaki da rashawa ta rufe gidan tsohon gwamna Kwankwaso a Kano Hoto: BBC.com
Asali: UGC

Jaridar ta kuma ruwaito cewa a lokacin da ta ziyarci yankin, daya daga cikin wadanda ke kusa lokacin da jami’an EFCC suka zo don rufe ginin ya yi tsokaci.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Hukumar kula da ayyukan 'yan sanda ta kafa sabon kwamitin binciken Abba Kyari

Ya bayyana cewa jami'an sun shaida musu cewa rufewar ya biyo bayan wata takardar korafi da hukumar ta samu daga iyalan Ismaila Gwarzo, tsohon mai ba da shawara kan harkokin tsaro.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Majiyar ta ce:

"Batun rufe gidan ya kasance lamari ne na kashin kansa tsakanin 'yan gidan Ismaila Gwarzo kuma Kwankwaso ya shiga cikin lamarin ne saboda shi ya siya daya daga cikin kadarorin."

Zuwa yanzu dai ba a ji ta bakin hukumar yaki da rashawar ba kan wannan sabon lamari.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito a baya cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawar na binciken tsohon gwamnan bisa zargin karkatar da kudaden kananan hukumomi da suka kai biliyan N3.08.

Mai magana da yawun hukumar ta EFCC, Wilson Uwujaren, ya tabbatar wa jaridar cewa hukumar na binciken zarge -zargen da ke cikin takardar korafi.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Hukumar EFCC Ta Cafke Tsohon Gwamna da Ta Jima Tana Nema a Filin Jirgi

Ta fasu: Magu ya hana bincikar Fintiri da wasu tsoffin gwamnoni 3, Kwamitin Salami

A gefe guda, mun kawo a baya cewa an zargi Ibrahim Mag da kange wasu bincike na zargin rashawa da ake wa wani gwamna mai ci yanzu da wasu tsoffin gwamnoni uku.

Kwamitin Jastis Ayo Salami ya ce yayin da Magu ke shugabantar EFCC, Magu "ya umarci jami'ai da kada su bincike" kan zargiin rashawa kan wasu mutum hudu, TheCable ta ruwaito.

Tsoffin gwamnonin an gano sun hada da Rabiu Musa Kwankwaso na jihar Kano, Donald Duke na jihar Cross River da Ibikunle Amosun na jihar Ogun wanda yanzu haka sanata ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng