Da duminsa: Hukumar kula da ayyukan 'yan sanda ta kafa sabon kwamitin binciken Abba Kyari

Da duminsa: Hukumar kula da ayyukan 'yan sanda ta kafa sabon kwamitin binciken Abba Kyari

  • Hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda ta kafa kwamitin cikin gida don bincike a kan laifin da FBI ta Amurka ke zargin DCP Abba Kyari ya aikata
  • Ana zargin Kyari, wanda tsohon shugaban IRT ne da laifin karbar rashawa daga hannun wani kasurgumin dan damfarar yanar gizo, Hushpuppi
  • Sakataren hukumar na kasa, Alhaji Abubakar Ismaila, ya rantsar da kwamitin kuma an kafa kwamitin ne musamman don zurfafa binciken

FCT, Abuja - Hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda ta kafa wata sabuwar kwamiti ta cikin gida wacce za ta yi bincike mai zurfi a kan takaddun da FBI ta Amurka ta gabatar wadanda suka janyo dakatar da mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, Abba Kyari.

Daily Trust ta ruwaito cewa, ana zargin Kyari, wanda shine tsohon shugaban IRT da amsar rashawa daga hannun wani rikakken dan damfarar yanar gizo, Abbas Ramon wanda aka fi sani da Hushpuppi.

Kara karanta wannan

Kotu ta yankewa barawon Al-kur'ani hukucin sharan masallaci na kwanaki 30 a Kano

Da duminsa: Hukumar kula da ayyukan 'yan sanda ta kafa sabon kwamitin binciken Abba Kyari
Da duminsa: Hukumar kula da ayyukan 'yan sanda ta kafa sabon kwamitin binciken Abba Kyari. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Daily Trust ta ruwaito yadda Kwamitin bincike na ‘yan sanda wacce sifeta janar na ‘yan sanda, Alkali Baba da mataimakinsa Joseph Egbunike suke shugabanta ta samar da kwamitin cikin gida.

Barista Tijjani Mohammed, shugaban bangaren hukunta ‘yan sanda ne ya kirkiri kwamitin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sakataren hukumar, Alhaji Abubakar Ismaila ne ya rantsar da kwamitin.

Karin bayani na nan tafe...

Hankalin ISWAP ya tashi, sun sauya tsarin shugabanci yayin da Boko Haram ke tuba

Mayakan ISWAP na Najeriya sun canja tsarin shugabancinsu da kungiyar masu basu shawarwari akan yadda mayakan Boko Haram da dama suka zubar da makamansu ga sojojin Najeriya.

Kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito, an tumbuke shugabannin ne bisa umarnin hedkwatar ISIS na Iraq da Syria, bisa kasa tabbatar da hadin kan ISWAP da mayakan Boko Haram bayan mutuwar Abubakar Shekau.

Kara karanta wannan

Ku Tuba Ku Miƙo Makamanku, Ko Ku Fuskanci Ƙalubale, Sabon Kwamishinan Ƴan Sandan Zamfara

Aba-Ibrahim ne ya maye gurbin Abbah-Gana wanda aka dauka a matsayin shugaban ISWAP, sai Malam Bako, Abdul-Kaka wanda aka fi sani da Sa’ad, Abu Ayun da Abba Kaka, su ne sababbin wadanda aka dauka a kungiyar masu bayar da shawara na ISWAP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel