Hotuna da bidiyoyin shagalin saka lallen auren Yusuf Buhari da Gimbiya Zahra Bayero

Hotuna da bidiyoyin shagalin saka lallen auren Yusuf Buhari da Gimbiya Zahra Bayero

  • Bikin gidan shugaban kasa Muhammadu Buhari da na gidan Sarkin Bichi, Alhaji Nasir Ado Bayero yana cigaba da daukan kala
  • A jiya Talata ne aka yi kayatacciyar liyafar saka lalle na amarya Gimbiya Zahra Bayero da Yusuf Muhammadu Buhari
  • Babu shakka hotuna da bidiyoyin tsarin wurin kadai ya isa ya kayatar da mai kallo balle kuma a kai ga wadanda suka halarta liyafar

Kano - Biki yayi biki, ana cigaba da shagulgula tare da shirin bikin gidan shugaban kasa da na masarautar Bichi.

A jiya Talata ne aka yi kayatacciyar liyafar saka lalle wacce aka yi domin bikin Gimbiya Zahra Bayero da kuma da namiji tilo na shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Hotuna da bidiyoyin shagalin saka lallen auren Yusuf Buhari da Gimbiya Zahra Bayero
Hotuna da bidiyoyin shagalin saka lallen auren Yusuf Buhari da Gimbiya Zahra Bayero. Hoto daga @thebeginningofyz
Asali: Instagram

Kamar yadda bidiyoyin da suka bayyana suka nuna, an yi saka lallen ne a wani irin nau'in wuri da ya sha kawa sannan kuma ba mai haske sosai ba.

Kara karanta wannan

Kyawawan Hotuna da bidiyon kafin aure na Yusuf Buhari da Gimbiya Zahra Bayero

Wurin an kawata shi da wasu launikan haske wadanda suka dace da kidan dake tashi sannu a hankali a wurin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yanayin tsarin wurin tare da kayatar dashi da aka yi da ado ya matukar dacewa da bikin manyan mutane.

Hakazalika, kawaye da 'yan uwan amarya Zahra Bayero basu bata kunya ba domin kowacce ta ci ado isasshe wanda ya dace da tsarin wurin.

@arewafamilyweddings sun wallafa bidiyoyi wadanda suka nuna tsarin wurin tare da kawayen amarya Zahra.

Za a daura auren Gimbiya Zahra Nasir Bayero da Yusuf Muhammadu Buhari, da daya namiji tilo na shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Juma'a mai zuwa.

Kyawawan Hotuna da bidiyon kafin aure na Yusuf Buhari da Gimbiya Zahra Bayero

Kyawawan hotunan kafin aure na Yusuf Muhammadu Buhari da Gimbiya Zahra Nasir Bayero sun fara bayyana a kafar sada zumuntar zamani ta Instagram.

Kara karanta wannan

Kisan matafiya a Jos: Sako mai ratsa zuciya da Ahmed Musa ya aikewa gwamnati

Ana ta shirin bikin da daya namiji tilo na gidan shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da Gimbiya Zahra, diya ga sarkin Bichi a jihar Kano.

Kamar yadda hotuna tare da bidiyo da suka fara bayyana na kafin bikin suka nuna, babu shakka auren soyayya ne za a kulla tsakanin diyar basaraken da dan shugaban kasan.

A daren Talata ne wurin daukar hoto mai suna @wraith_studios dake Abuja suka wallafa kyawawan hotunan kyakyawar amarya Zahra tare da angonta.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel