An harbe dan sanda har lahira yayin da 'yan bindiga suka sace jami'in kwastam a Taraba
- Wasu ‘yan bindiga sun halaka jami’in dan sanda sannan suka sace wani babban jami’in kwastam a Jalingo, babban birnin jihar Taraba
- Maharan sun kai farmaki gidan jami’in kwastam din mai suna Abbas Bello da tsakar dare
- Mai magana da yawun 'yan sandan jihar, DSP Abdullahi Usman, ya tabbatar da faruwar lamarin
Rahotanni sun kawo cewa wasu ‘yan bindiga sun kashe jami’in dan sanda yayin da suka yi awon gaba da wani babban jami’in kwastam a Jalingo, babban birnin jihar Taraba.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ‘yan bindigar sun mamaye gidan jami’in kwastam din mai suna Abbas Bello da misalin karfe 2:00am na ranar Alhamis, 19 ga watan Agusta.
An tattaro cewa sun yi artabu da 'yan sanda inda suka yi musayar wuta, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar wani sajen.
An kuma ce wani sifeton 'yan sanda ya samu rauni a yayin harin.
An bayyana jami'in da aka kashe a matsayin Sajan Ogedi Habu yayin da wanda aka raunata ya kasance sifeto Ibrahim Joseph.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Abdullahi Usman, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, Abimbola Sokoya, ya ziyarci iyalan jami’in kwastan da aka sace.
A wani labari, kira ga kare kai da Gwamna Bello Masari yayi wa mazauna Katsina ya samu goyon baya daga wasu kungiyoyin al'adu na arewacin kasar, wanda daya daga cikinsu ita ce Arewa Consultative Forum (ACF).
Kungiyar ta ce Masari ya yi daidai da ya roki mutanensa da su dauki makamai don yaki da 'yan fashi da masu garkuwa da mutane, ta kara da cewa ba dukkan makamai ne suka zama haramun ga yan kasa ba, musamman wadanda ke zuwa da izinin 'yan sanda.
Asali: Legit.ng