Nadin mukamai: Murna ta koma ciki, tsohon Kwamishina ya ga samu, ya ga rashi a Bauchi

Nadin mukamai: Murna ta koma ciki, tsohon Kwamishina ya ga samu, ya ga rashi a Bauchi

  • Bala Abdulqadir Mohammed ya tura wa Majalisa sunayen sabbabin Kwamishinoni
  • Da farko an ga sunan Samaila Burga a cikin wadanda za a ba kujerar Kwamishinan
  • Rahotonni sun ce Gwamnan Bauchi ya cire sunan tsohon Kwamishinan daga baya

Bauchi - Mai girma gwamnan jihar Bauchi, Bala Abdulqadir Mohammed, ya janye sunan daya daga cikin wadanda ya zaba zai ba kujerar Kwamishina.

An cire sunan Samaila Burga bayan sa'a 24

Punch ta kawo rahoto cewa gwamnatin Bauchi ta cire Samaila Burga daga jerin sababbin kwamishinoninta.

Kamar yadda muka samu labari, da farko Mista Samaila Burga yana cikin wadanda suka samu shiga jerin sababbin kwamishinoni 17 da gwamna ya fitar.

Sanata Bala Abdulqadir Mohammed ya aika sunayen wasu zuwa gaban ‘yan majalisar dokokin jiha, yana sa rai a tantance su domin a tabbatar da nadinsu.

Kara karanta wannan

Bidiyo ya bayyana yayin da APC ke rabawa gwamnoni manyan mukamai

Gwamna Bala Mohammed ya tura sunayen kwamishinonin da yake so ya yi aiki da su ga shugaban majalisar dokokin Bauchi, Rt. Hon. Abubakar Suleiman.

Meyasa aka janye sunan Burga?

Tribune ta ce a jerin farko da ya fita, tsohon kwamishinan harkar gona, Burga ya dawo cikin kwamishinoni da gwamnan zai sake nada wa a wannan karo.

Gwamnan Bauchi
Sanata Bala A. Mohammed Hoto: wikkitimes.com
Asali: UGC

Karamar hukumar Tafawa-Balewa ce kurum ta samu mutane biyu a kujerun, domin kuwa bayan Sulaiman Burga, akwai sunan Abubakar Abdulhamid Bununu.

Kwatsam, sai aka samu labari daga baya cewa Mai girma gwamna ya cire sunan tsohon kwamishinan na sa daga cikin wadanda majalisa za ta tantance.

Rahoton yace gwamnan bai bada dalilin cire sunan Samaila Burga ba. Da wannan mataki, babu wata karamar hukuma da ta samu wakilcin mutum fiye da daya.

Kara karanta wannan

Goggo: Gwamnatin Jihar Kano ta musanya rade-radin cewa ‘Murtala Garo zai gaji Ganduje a 2023’

Za a sa rana domin a samu lokacin da za a tantance majalisar. Shugaban masu rinjaye aka ba alhakin tuntubar gwamna domin a kawo takardun wadanda ya zakulo.

Su wanene sababbin Kwamishinonin?

Ga jerin kwamishinonin da ake sa rai nan kamar yadda Abdul Ahmad Burra ya sanar.

Alkaleri: Abdulkadir Ibrahim

Bauchi: Garba Dahiru

Bauchi: Nuruddeen Abdulhamid

Dambam: Ahmed Aliyu Jalam

Darazo: Dayyabu Chiroma

Dass: Maryam Garba Bagel

Gamawa: Umar Babayo Kesa

Giade: Asma'u Ahmed

Jama'are: Usman Abdulkadir Moddibo

Itas - Gadau: Hajara Jibrin Gidado

Katagum: Sama'ila Dahuwa Kaila

Misau: Aminu Hammayo

Shira: Hamisu Muazu Shira

Tafawa Balewa: Abubakar Abdulhamid Bununu

Toro: Aliyu Usman Tilde

Warji: Abdulrazak Nuhu Zaki

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng