Abubuwa 4 Muhimmai Da Na Ke Ƙaunar Aikatawa a Rayuwata, Sarkin Bichi Kuma Sirikin Buhari

Abubuwa 4 Muhimmai Da Na Ke Ƙaunar Aikatawa a Rayuwata, Sarkin Bichi Kuma Sirikin Buhari

  • Mai martaba sarkin Bichi, sirikin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana abubuwa 4 da yake matukar so
  • A wani bidiyo wanda aka tattauna dashi, ya bayyana yadda yake matukar son kadaici a rayuwarsa
  • A cewarsa, yana matukar son karatu da tafiye- tafiye don hakan yana matukar nishadantar dashi

Bichi, Kano - Sarkin Bichi, Mai Martaba Alhaji Nasir Ado Bayero, sirikin shugaban kasa Muhammadu Buhari, a wani bidiyon tattaunawa dashi da wakilin Daily Trust ya yi ya bayyana abubuwa 4 da yake matukar sonyi a rayuwarsa.

1. Da farko ya bayyana cewa yana matukar son kadaici ba tare da wani ya dame shi ba. Yana son kadaice kansa daga cikin mutane.

Abubuwa 4 Muhimmai da Nake Kaunar Aikatawa a Rayuwata, Sarkin Bichi Kuma Sirikin Buhari
Abubuwa 4 Muhimmai da Nake Kaunar Aikatawa a Rayuwata, Sarkin Bichi Kuma Sirikin Buhari. Hoto daga Masarautar Kano
Asali: Facebook

Ina matukar son kasancewa ni daya saboda hakan yana bani damar yin tunani mai zurfi akan abubuwan da nayi da wadanda nake son yi a nan gaba. Saboda idan kana cikin mutane, yin tunani yana da matukar wahala don haka kasancewa kai daya zai iya baka damar samar da wani sabon abu. Ni dai ina son zama ni kadai sosai, a cewar Sarkin.

Kara karanta wannan

A karshe kungiyar Arewa ta bayyana wanda Boko Haram suke tsoro fiye da 'yan sanda da sojoji

2. Sarkin ya bayyana cewa yana matukar son karatu don shi makaranci ne.

A cewarsa:

Ina matukar son yin karatu kuma ina karanta duk littafin da na samu. Ina karatu kullum, idan na kusa yin bacci akwai littafin da zan karanta,” inji Sarkin Bichi.

3. Sarkin ya bayyana yadda yake son yin tafiye-tafiye duk da dai yanzu baya iya yin tafiye-tafiyen kamar da. Amma yana matukar son ziyartar wurare iri-iri. Sarkin ya ce idan ya yi tafiyar yana son kasancewa cikin kadaici.

4. A cewar mai martata, idan ya samu lokaci yana son yin tattaki saboda ya gaji hakan a wurin mahaifinsa ne, Daily Trust ta ruwaito.

Sun kasance suna yin tattaki da mahaifinsa na tsawon sa'o'i 2 zuwa uku tare, idan suka gaji sai su nemi wuri su huta su sha ruwa, tukunna sai su mike su cigaba da tafiyar.

Kara karanta wannan

Hamshakin biloniya ya rasa diyarsa, watanni 2 bayan dan shi ya sheke kansa

Kuma har yanzu bai bar wannan sunnar mahaifin tasa ba, ya kasance yana yi har yanzu idan ya samu dama. A cewarsa ko jihar Legas yaje yana yin tattakin nan idan ya samu dama.

Gwamnatin Kaduna Ta Bayyana Ranar Buɗe Makarantu, Ta Sanya Wa Ɗalibai Sabon Ƙa’ida

A wani labari na daban, gwamnatin Jihar Kaduna ta sanar da cewa za ta fara bude makarantu daga ranar Laraba, 18 ga watan Agustan shekarar 2021, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Sai, dai tace daliban da ke karamin aji na 3 wato JSS III ne kadai za su koma makarantun.

A cewar rahoton da Daily Trust, Kwamishinan ilimi na jihar Kaduna, Shehu Usman Muhammad ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel