Da kaca aka daure Igboho a Cotonou don gudun kada ya zama Mage ya tsere, Lauyansa

Da kaca aka daure Igboho a Cotonou don gudun kada ya zama Mage ya tsere, Lauyansa

  • Daya daga cikin lauyoyin Sunday Igboho ya bayyana yadda ‘yan sandan jamhuriyar Benin suka daure Igboho da kaca
  • A cewar lauyan, ‘yan sandan sun daure shi ne don gudun ya rikida ya koma mage kuma ya tsere bayan kama shi da suka yi a filin jirgin
  • A cewar Falola, ‘yan sandan sun yi fargabar kada ya sauya halitta cikin kankanin lokaci saboda tsananin karfin bakin tsafinsa

Cotonou - Daya daga cikin lauyoyin mai assasa samar da kasar Yarabawa, Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Igboho ya bayyana yadda ‘yan sandan jamhuriyar Benin suka daddaure Igboho da kaca don gudun kada ya rikida ya koma mage kuma ya tsere daga hannunsu a filin jirgin kasar.

Kamar yadda saharareporters suka ruwaito, Olusegun Falola ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai wa Igboho ziyara a inda aka tsare shi.

Kara karanta wannan

Kisan matafiya a Filato: Yadda Kiristoci, 'yan adaidaita da sojoji suka cece mu, Matafiyi

A cewar Falola, jami’an ‘yan sandan sun ji tsoron ya bace a cikin iska saboda bakin tsafinsa mai cike da al’ajabi.

Da kaca aka daure Igboho a Cotonou don gudun ya zama Mage ya tsere, Lauyansa
Da kaca aka daure Igboho a Cotonou don gudun ya zama Mage ya tsere, Lauyansa. Hoto daga saharareporters.com
Asali: UGC

A cewar lauyan:

Lokacin da na isa inda aka tsare Igboho da farko, na gan shi daure da kaca ne. Sun ji tsoron yayi fitar iska ya bace sakamakon tsabar siddabarunsa.
'Yan sandan sun sanar dani cewa idan aka cire kacar kuma Igboho yayi tsafi ya bace, ya yarda a cire shi daga matsayinsa kuma a fatattake shi daga aikin dan sanda.
Dan sandan ya ce an sanar dasu cewa Igboho zai iya komawa mage ko kuma wani abun daban, shiyasa suka daddaure shi da kaca.

Kamar yadda shafin Linda Ikeji ya wallafa, ya sanar da cewa saida yasa baki cikin gaggawa kafin aka kwance mishi daurin da aka yi mishi.

Kara karanta wannan

Abokin kirki: El-Rufa'i ya tuna yadda ya hadu da tsohon sarkin Kano Sanusi a jami'a

Gwamnatin tarayya zata ci bashin N4.89trn don daukar nauyin kasafin 2022

A wani labari na daban, gwamnatin tarayya ta bayyana kudirinta na amso rancen cikin gida da na waje na naira tiriliyan 4.89 don samar da kudaden kasafin shekarar 2022 na naira tiriliyan 5.62.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Ministar kudi ta bayyana wannan kudirin a wata takarda da ta mika ga ma’aikatarta ne ga majalisar wakilai ta MTEF da FSP na 2022 zuwa 2024 a ranar Litinin.

Ministar ma’aikatar kudi, kasafi da tsare-tsaren kasa, Zainab Ahmed, a gabatarwar da tayi ta ce gwamnatin tarayya za ta rage yawan kudaden da take narkawa ma’aikatu, sasanni da hukumomi da naira biliyan 259.31.

Asali: Legit.ng

Online view pixel