Muna kashe N8m kulli yaumin wajen ciyar da dalibai a jihar Enugu, Minista Sadiya
- Gwamnatin tarayya ta bayyana makudan kudin da take kashewa daliban firamare kullum a Enugu
- Wannan na shirin tsarin ciyar da daliban firamare da gwamnati keyi a fadin tarayya
- Ministar ma'aikatar walwala da jin dadin al'umma ta ce gwamnati zata cigaba da ciyar da dalibai
Enugu - Gwamnatin tarayya tace tana kashe milyan takwas kulli yaumin kan dalibai 114,261 don ciyar da su karkashin shirin ciyar da daliban makaranta a jihar Enugu.
Ministar manajin annoba da jin dadin al'umma, Sadiya Umar Farouq, ta bayyana hakan ranar Litinin a Abuja.
Minista Sadiya, wacce ta samu wakilcin jagorar lura da shirin na jihar Enugu, Ms Adanne Wadibia-Anyanwu, ta kara da cewa gwamnatin ta dauki masu girki 1,532 dake girkawa daliban firamare abinci a jihar.
Wannan na kunshe cikin jawabin da mai magana da yawunta, Nnema Iken Anibeze, Sun ta ruwaito.
Tace:
"Gwamnatin tarayya na kashe kimanin N7,998,270 wajen ciyar da dalibai 114,261 a makarantun firamare gwamnati dake cikin jihar."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Wannan shiri ya taimakawa yan makarantun firamare a makarantun gwamnati 799 dake kananan hukumomin jihar 17."
"Mun zo ne domin samun karin bayani kan shirin. Muna tattara bayanan daliban da ake ciyarwa ne da kuma samun bayanai daga masu girki da shugabannin makarantu."
Mun kashe kimanin bilyan 2 wajen ciyar da daliban firamare a jihar Ondo, gwamnatin tarayya
Gwamnatin tarayya ta ce ta kashe kudi N1.8bn wajen ciyar daliban makarantun a jihar Ondo kadai cikin shekaru uku.
Ministar manajin annoba da jin dadin jama'a, Sadiya Umar Farouq, ta bayyana hakan lokacin taron daukar sunaye da hotunan dalibai a jiihar Ondo.
Ta ce kawo yanzu akwai sunayen dalibai 108,842 a cikin runbun bayanan kuma ta lashi takobin ci gaba da hakan don tattara bayanan yaran da ake ciyarwa.
Ministar ta tabbatar da cewa kawo yanzu an kashe N1.8bn cikin shekaru uku da suka gabata don ciyar da dalibai a jihar Ondo karkashin shirin NHGSF.
Asali: Legit.ng