'Yan Bindiga Sun Afka Gidajen Mutane Da Tsakar Dare, Sun Sace Manya Da Yara a Niger

'Yan Bindiga Sun Afka Gidajen Mutane Da Tsakar Dare, Sun Sace Manya Da Yara a Niger

  • Yan bindiga sun afka gidajen mutane da tsakar dare a Kwankwashe a Suleja a jihar Niger
  • Maharan sun sace mutane a kalla biyar cikinsu har da yar shekara 17 da dan shekara 15
  • Mazaunan unguwar da dama sun tabbatar da harin sun kuma bayyana ababen da yan bindigan suka sace musu

Suleja, Jihar Niger - Yan bindiga sun kai hari garin Kwankwashe da ke kan hanyar Suleja zuwa Madalla, a jihar Niger a safiyar ranar Laraba sun sace mutane ciki har da yara, Daily Trust ta ruwaito.

Wani shaidan gani da ido ya ce an sace mutane daga gidaje uku da kuma wani otel da ke Unguwar Fulani a yankin.

'Yan Bindiga Sun Afka Gidajen Mutane Da Tsakar Dare, Sun Sace Manya Da Yara a Niger
Wani gida da yan bindiga suka kai hari suka sace yara a Niger. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Abin da mazauna unguwar suka ce game da harin?

Wata yar unguwar, Faith Lucky, wacce aka sace yaranta biyu, yarinya mai shekara 17 da yaro mai shekara 15, ta ce ta gane cewa sun iso gidanta ne yayin da suka fara buga kofar shiga gidan.

Ta ce sun dauki kimanin minti 20 kafin suka balle kofan gidanta.

A cewarta:

"Na tada yara na daga barci na yi yunkurin turasu su fice ta tagan daki na, amma cikin kankanin lokaci sai suka taho wurin suka balle wani sashi na tagar.
"Suka haska tocila, suka nuna min bindiga suka ce in bude kofar dakin."

Matar ta kara da cewa sun tilasta musu bada wayoyinsu tare da dukkan kudaden da suke da shi a hannunsu kafin suka tafi da yaranta biyu.

Wata matar daban ta ce yan bindigan sun isa gidanta misalin karfe 1 na dare, amma ita da mijinta sun tsere.

Amma ta ce maharan sun yi nasarar isa inda surukanta da ta kawo musu ziyara ta ke.

Matar ta ce:

"Suruki na ya tsaya tare da mama saboda ba za ta iya guduwa ba. Hakan yasa suka tafi da shi sannan suka sace kayan mu kamar wayar salula, laptop, tufafi da takalma."

Wani mazaunin unguwar da yace sunansa Ruben, ya ce maharan sun kuma sace wasu ma'aikatan otel biyu a yankin, ya kara da cewa sun dauki kimanin awa daya suna sata kafin suka tsere bayan sun ji karar jiniyan motar yan sanda.

An yi kokarin ji ta bakin Kwamandan yan sandan yankin Suleja, ACP Sani Badarwa a lokacin hada wannan rahoton amma hakan bai yiwu ba.

An Kama Matar Ɗan Bindiga a Katsina Da N2.4m, Mijin Ya Tsere Ya Bar Ta

A wani labarin, yan sanda a jihar Katsina sun kama wata matar aure, Aisha Nura, mai shekaru 27 dauke da kudi Naira miliyan 2.4 na cinikin makamai da aka sayarwa yan bindiga, The Punch ta ruwaito.

An kama Aisha, da aka ce matar dan bindiga ne, a ranar 25 ga watan Yuli a yayin da ta ke shirin hawa kan babur din haya (acaba) daga Batsari zuwa kauyen Nahuta.

Mai magana da yawun yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya tabbatar da hakan a ranar Juma'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel