Yakasai: Abin Da Yasa Na Shiga Damuwa Kan Gayyatar Da EFCC Ta Yi Wa Bukola Saraki

Yakasai: Abin Da Yasa Na Shiga Damuwa Kan Gayyatar Da EFCC Ta Yi Wa Bukola Saraki

Dattijon dan kasa, Alhaji Tanko Yakasai ya nuna damuwarsa kan gayyatar da EFCC ta yi wa Bukola Saraki

Tanko Yakasai ya bayyana cewa baya nufin yi wa doka katsalandan amma ya damu domin akwai yiwuar gayyatar na da alaka da siyasar 2023

Yakasai ya ce Bukola tamkar da ne a gare shi domin dan tsohon abokinsa ne Dr Olusola Saraki kuma Bukola abokin babban dansa ne

Alhaji Tanko Yakasai, Dattijon Dan Kasa, a ranar Litinin ya ce akwai yiwwar gayyatar da EFCC ta yi wa tsohon shugaban majalisa Bukola Saraki na da alaka da siyasa, Daily Trust ta ruwaito.

Da ya ke magana a Kano, Yakasai ya ce akwai yiwuwar gayyatan yunkuri ne na karya wa tsohon shugaban majalisar gwiwa don kada ya yi takarar shugaban kasa a 2023 kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Yakasai: Abin Da Yasa Na Shiga Damuwa Kan Gayyatar Da EFCC Ta Yi Wa Bukola Saraki
Yakasai: Abin Da Yasa Na Shiga Damuwa Kan Gayyatar Da EFCC Ta Yi Wa Bukola Saraki. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Saraki tamkar da ya ke a gare ni, Tanko Yakasai

Kara karanta wannan

Dattijon Arewa ya fadi ainihin dalilin da ya sa EFCC ta sake biyowa ta kan Bukola Saraki

Ya ce abin ya dame shi domin Saraki tamkar da ya ke a gare shi.

Ya ce, "Na karanta rahoto a sociyal midiya EFCC ta gayyaci da na kuma dan aboki na marigayi, Dr Olusola Saraki a ranar Asabar da ta gabata 31 ga watan Yulin 2021.
"Ba zan so in yi katsalandan cikin ayyukan jami'an tsaro ba. Amma, ina fata wannan gayyatar da EFCC ta yi wa tsohon shugaban majalisar dattawar ba ta da alaka da siyasa ko zaben da ke tafe a kasar mu.
"Bukola da na ne daga bangarori daban-daban, dan tsohon aboki na ne, shugaban majalisa a jamhuriya ta biyu, marigayi Dr Olusola Saraki. Kuma Bukola abokin babban da na ne.
"Saboda wannan dalilin, na kan damu don lokacin da naga ana neman matsa masa. Bugu da kari, a matsayina na wanda ya mayar da hankali wurin kare hakkin bil adama da walwala a kasar ko da yara na bane ko yaran abokai na da yan uwa na. Na shafe kimanin shekaru 70 ina wannan gwagwarmayar.

Kara karanta wannan

An daure shugaban matasan PDP a gidan yari saboda ya zagi Buhari, SGF a Facebook

"Ina fatan wannan ba wani mataki ne na musguwnawa Saraki a siyasaance ba daga wadanda suke jam'iyyar da ke mulki. Ba na cikin kowanne jam'iyya a Nigeria, don hakan wannan maganan da na yi yunkuri ne na kare dukkan yan Nigeria ba tare da la'akari da matsayi, kabila ko siyasa ba."

Dangi da 'yan uwa na saka 'yan siyasa satar kuɗin gwamnati, Ministan Buhari

A wani labarin daban, karamin ministan Kwadago da Samar da Ayyuka, Festus Keyamo SAN, ya ce matsin lamba da yan uwa da abokai ke yi wa mutane da ke rike da mulki ne neman su basu kudi ne ka karfafa musu gwiwa suna sata da aikata rashawa.

A cewar The Sun, Keyamo ya yi wannan furucin ne yayin jawabin da ya yi a ranar Laraba a Abuja yayin kaddamar da shirin 'Corruption Tori Season 2' da Signature TV da gidauniyar MacArthur suke daukan nauyi.

Kara karanta wannan

Rudani a Kano bayan majalisar jiha ta gayyaci shugaban alkalai kan shari'ar Rimingado

An kirkiri shirin ne domin wayar da kan mutane game da rawar da za su iya takawa wurin yaki da rashawa da cin hanci a Nigeria ta hanyar amfani da harsunan mutanen Nigeria.

Asali: Legit.ng

Online view pixel