Hujjojin da Aka Kawo Sun Mun Tsauri, Alkalin Kotu Ya Dage Sauraron Karar Sheikh Abduljabbar
- Kotun shari'ar musulunci dake Kano ta dage sauraron shari'ar Sheikh Abduljabbar Kabara
- Alkalin kotun, Ibrahim Sarki Yola, ya bukaci a bashi lokaci ya yi nazari a akan hujjojin da kowane ɓangare ya gabatar
- A zaman na ranar Laraba, bangaren gwamnati ya gabatar da sabbin tuhume-tuhume kan shehin Malamin
Kano - Alkalin dake jagorantar shari'ar Sheikh Abduljabbar Kabara da gwamnatin Kano, Ibrahim Sarki Yola, ya ɗage sauraron karar zuwa 2 ga watan Satunba.
Yola ya bayyana cewa hujjojin da lauyoyi suka gabatar a gabansa a zaman kotu na ranar Laraba suna da sarkakiya kuma suna bukatar dogon nazari, kamar yadda daily nigerian ta ruwaito.
A cewarsa zai yi nazari a kan abinda ya dace game da sabbin tuhume-tuhume da ɓangaren gwamnati ya sake gabatarwa game da malamin.
Ya zaman kotun ya kasance?
BBC Hausa ta ruwaito cewa a zaman da kotun ta yi ranar Laraba, an tsaurara tsaro fiye da zaman baya.
An yi takaddama tsakanin lauyoyin gwamnati da kuma masu kare Malam Abduljabbar game da wata takardar sabbin tuhuma da gwamnati ta gabatar.
Shugaban majalisar lauyoyin dake kare Abduljabbar, Saleh Bakaro, ya soki matakin gwamnati na dakko lauyoyi masu darajar SAN.
Bakaro yace lauyoyi SAN ba su da ikon shiga karamar kotu a tsarin dokokin aikin Lauya, sai dai babbar kotun tarayya.
Bakaro yace:
"Sabbin tuhumar da suka gabatar wa Kotu ya sabawa shari'ar musulunci, hakanan kuma lauyoyin SAN basu da iko shiga karamar Kotu."
Sai dai a ɓangaren gwamnati, Barista Surajo Sa'id SAN, yace bai kamata lauyoyin Abduljabbar su yi katsalandan ba yayin da ake gabatar da tuhume-tuhume ga Alkali.
Lauyan ya kara da cewa doka ta wajabta kammala gabatar da tuhuma kafin wani ɓangare ya amince ko ya soki abinda aka gabatar.
Wane mataki Alkali ya dauka?
Bayan doguwar muhawara da aka gabatar da hujjoji daga kowane ɓangare, Alkali Yola, ya bayyana cewa zai yi nazari a kan hujjojin kowane ɓangare da kuma sabbin tuhumar da gwamnati ke son karawa.
Alkalin yace zai ɗauki wannan matakin ne domin tabbatar da adalci a aikinsa, daga nan ya ɗage sauraron karar zuwa 2 ga Satumba.
A wani labarin kuma Duk Mai Son Gani Bayan IMN Zai Sha Kunya, Sheikh Zakzaky Ya Yi Jawabi Na Farko Bayan Shakar Iskar Yanci
Shugaban kungiyar mabiya akidar shi'a (IMN), Sheikh IbrahIm El-Zakzaky, ranar Talata yace duk mai son wargaza tafiyarsa ba zai ci nasara ba.
Malamin yace duk wata bita da kulli da akewa kungiyar IMN, wanda ya jawo aka tsare shi tsawon shekara 6, ba abinda zai kara wa kungiyar sai farin jini a idon duniya.
Asali: Legit.ng