Duk Mai Son Gani Bayan IMN Zai Sha Kunya, Sheikh Zakzaky Ya Yi Jawabi Na Farko Bayan Shakar Iskar Yanci
- Shugaban IMN, Sheikh Ibrahim Zakzaky, ya gana da wakilan kungiyarsa da wasu kungiyoyi a Abuja
- Karon farko bayan fitowarsa daga kurkuku, Zakzaky yace duk kokarin tarwatsa tafiyar shi'a ba zai samu nasara ba
- Malamin ya kuma yi ta'aziyya ga mabiyansa bisa lamarin da ya faru tsakaninsu da sojoji a 2015
Abuja - Shugaban kungiyar mabiya akidar shi'a (IMN), Sheikh IbrahIm El-Zakzaky, ranar Talata yace duk mai son wargaza tafiyarsa ba zai ci nasara ba.
Zakzaky yayi wannan maganar ne a taronsa na farko da wakilan kungiyarsa na jihohi da wasu kungiyoyi a Abuja, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Malamin yace duk wata bita da kulli da akewa kungiyar IMN, wanda ya jawo aka tsare shi tsawon shekara 6, ba abinda zai kara wa kungiyar sai farin jini a idon duniya.
Mun fuskanci kalubale a 2015
Sheikh Zakzaky yace:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Ko da makiya sun ɗaura ɗamarar yakar mu, ba zasu sami nasara ba illa su kara ɗaukaka kungiyar mu zuwa wani matsayi da bamu yi tsammani ba."
"Lokacin da aka karkashe mu a Zaria a shekarar 2015 yana da wahalar jurewa domin ya shafi mutane da dama."
Ya yabawa kungiyoyi da suka taimaka
Shehin malamin ya nuna jin daɗinsa ga kungiyoyin kare haƙkin ɗan adam na gida da waje bisa jajircewarsu wajen ganin an sake shi.
Hakanan ya gode wa mabiyansa waɗanda suka sadaukar da rayuwarsu, da waɗanda suka ji rauni duk dominsa, kamar yadda sahara reporters ta ruwaito.
Shugaban yan shi'a ya kuma yi ta'aziyya ga iyalan waɗanda suka rasa yan uwansu da masoyansu yayin rikici da sojoji a Husainiyya.
Ya kuma yi addu'an Allah ya jikansu da rahama yasa aljannar ta zama ita ce makomarsu.
A wani labarin kuma Mutum Daya Ya Mutu a Wani Gumurzu Tsakanin Sojoji da Yan Bindiga a Katsina
Wasu yan bindiga da sojojin kasar Nijar suna musayar wuta a bodar Jibiya, jihar Katsina
Rahotanni sun bayyana cewa yan ta'addan ne suka kai hari kauyukan dake kusa a Nijar, suka sato dabbobi.
Dan majalisa mai wakilar Jibiya, Mustapha Yusuf, yace sojojin sun biyo yan bindigan ne domin kwato dabbobin.
Asali: Legit.ng