Mutum Daya Ya Mutu a Wani Gumurzu Tsakanin Sojoji da Yan Bindiga a Katsina

Mutum Daya Ya Mutu a Wani Gumurzu Tsakanin Sojoji da Yan Bindiga a Katsina

  • Wasu yan bindiga da sojojin kasar Nijar suna musayar wuta a bodar Jibiya, jihar Katsina
  • Rahotanni sun bayyana cewa yan ta'addan ne suka kai hari kauyukan dake kusa a Nijar, suka sato dabbobi
  • Dan majalisa mai wakilar Jibiya, Mustapha Yusuf, yace sojojin sun biyo yan bindigan ne domin kwato dabbobin

Katsina- Yanzun haka sojojin Nijar da wasu gungun yan bindiga suna musayar wuta a bodar karamar hukumar Jibiya, jihar Katsina.

Premium Times ta ruwaito daga majiya da dama cewa yan bindigan sun kashe soja ɗaya, sun kwace motar yakin sojojin kasar Nijar a gumurzun da aka fara tun ranar Litinin.

Dan majalisa mai wakiltar Jibiya a majalisar dokokin Katsina, Mustapha Yusuf, ya bayyana cewa yan bindigan ne suka fara kutsawa kasar Nijar, inda suka sato dabbobi zuwa Najeriya.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Hallaka Mutum 4, Sun Yi Awon Gaba da Wasu da Dama a Jihar Katsina

Sojojin Jamhuriyar Nijar
Da Duminsa: Mutum Daya Ya Mututu Yayin da Yan Bindiga Suka budewa Sojoji Wuta a Bodar Katsina Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Meya kawo sojojin Nijar cikin Najeriya?

Honorabul Yusuf yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Sojojin jamhuriyar Nijar sun shigo Najeriya domin kuɓutar da wasu dabbobi biyo bayan harin da wasu yan bindiga suka kai kauyukan ƙasar."
"Ɗoka ta basu damar shigowa Najeriya har tsawon kilomita 30 matukar dalilin ya shafi tsaro."

Yusuf yace yan bindigan sun kashe sojan Nijar ɗaya sannan sun kwace motar yaki guda ɗaya bayan sun musu wani kwantan ɓauna.

Ya kara da cewa wasu sojojin jamhuriyar Nijar da dama tare da wani jagoran yan bijilanti sun bata tun ranar Litinin.

Wane hali mazauna yankin suke ciki?

Wasu mazauna yankin sun bayyana cewa sun ga motoci aƙalla 17 cike da sojojin Nijar sun nufi wani daji.

Jim kaɗan bayan wucewar sojin sai aka fara jiyo karar harbe-harbe wanda ake tsammanin sojojin ne suka buɗe wuta kan yan bindiga a dajin.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Allah ya yiwa Ibrahim Mantu, tsohon mataimakin shugaban majalisa rasuwa

Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Katsina, Gambo Isa, ya ƙi daga kiran wayar da ake ta masa domin jin ta bakinsa.

A wani labarin kuma kun ji cewa Wasu Yan Bindiga Sun Sake Kai Sabon Hari Jihar Kaduna

Aƙalla mutum uku suka rasa ransu a wani sabon hari da yan bindiga suka kai kauyen Gora Gida, karamar hukumar Zangon Kataf, jihar Kaduna.

Da yake magana da dailytrust, Hakimin Gora, Mr Elias Gora, yace yan bindiga sun kai harin ne da misalin karfe 11:00 na daren ranar Lahadi.

Ya kara da cewa wata mata ta samu raunin harbin bindiga sannan kuma maharan sun kona mota guda ɗaya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel