EFCC: Kotu ta ce a karbe N241m da aka karkakatar daga ofishin Hadimin Shugaba Buhari

EFCC: Kotu ta ce a karbe N241m da aka karkakatar daga ofishin Hadimin Shugaba Buhari

  • Kotun Tarayya da ke Legas ta ce hukumar EFCC ta rike wasu Naira miliyan 241
  • Lauyoyin EFCC suna zargin an yi gaba da wadannan kudin ne daga baitul-mali
  • Ana tuhumar Jami’an ofishin Mai ba shugaban kasa shawara a kan SDG da sata

Lagos - Wani babban kotun tarayya mai zama a garin Legas ya zartar da cewa a karbe wasu kudi da aka karkatar daga ofishin hadimin shugaban kasa.

Ana zargin an yi awon gaba da N241m

Alkali mai shari’a Nicholas Oweibo ya bada umarni a rike Naira miliyan 241 da aka yi gaba da su daga ofishin mai ba shugaban kasa shawara a kan SDG.

Jaridar The Nation ta ce Alkalin ya kuma yanke hukunci cewa a karbe wasu shaguna da ke kan layin Ekukinam, a unguwar Utako, birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Kotu ta garkame manajar banki shekara 5 kan satar kudin banki N4.8m

Nicholas Oweibo ya dauki wannan mataki ne bayan lauyan EFCC, Rotimi Oyedepo ya shigar da kara.

Yadda aka tafka ta'adi a ofishin SDG

Hukumar EFCC ta bakin Rotimi Oyedepo, ta fada wa kotu cewa an boye wadannan kudi ne kashi-kashi; N65m, N61m, N50, da N65 a wasu bankuna biyu.

EFCC tace bincikenta ya nuna mata cewa an saye wannan shaguna da ke Abuja ne da kudin da aka karkatar daga ofishin mai ba shugaban kasa shawara.

Shugaba Buhari
Shugaba Buhari a ofis Hoto: www.lindaikejisblog.com
Asali: UGC

Rahoton yace Abdulsalam Bawa ne babban akawu a ofishin hadimin shugaban Najeriyar. Ana zargin Bawa ya hada-kai da wasu ma’aikata aka yi satan.

Lauyan da ya tsaya wa gwamnati ya zargi wasu kamfanoni; Kouchdim Unity Nigeria Ltd da Lankass Global Ventures da hannu wajen wannan badakala.

“Mun bankado akwai wani gida da aka saya da dukiyar jama’a da aka wawura, Abdulsalam Bawa ya ci amanar da aka damka masa.”

Kara karanta wannan

GMD ya yi zazzaga a NNPC, an canza wa wasu manyan ma’aikata wuraren aiki, an tsige wani

Alkali Oweibo ya daga karar mai lamba ta FHC/L/CS/90/2021 zuwa 6 ga watan Satumba, 2021, domin a ji hukuncin karshe da za a yanke a kan dukiyoyin.

VAT: Gwamnatin Ribas ta doke FIRS a kotu

Gwamnatin tarayya ta samu N2.5tr daga VAT daga lokacin da aka kara haraji. Amma a wata shari’a da aka yi, an ce Jihohi ne ke da ikon karbar VAT dinsu.

Rahotanni sun nuna kudin shigan da gwamnatin tarayya ke samu zai ragu a sakamakon hukuncin, amma kamar FIRS za ta daukaka kara a babban kotu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng