PSG: Za ka iya fara zama a gidana – Sergio Ramos ya tarbi Lionel Messi hannu biyu-biyu

PSG: Za ka iya fara zama a gidana – Sergio Ramos ya tarbi Lionel Messi hannu biyu-biyu

  • Sergio Ramos ya fada wa Lionel Messi cewa zai iya fara zama a gidansa
  • Tsohon ‘Dan wasan na Real Madrid ya koma abokin Lionel Messi a PSG
  • A lokacin da ‘Yan wasan suke kasar Sifen, sun kasance 'yan adawan juna

Paris - A makon nan ne babban ‘dan wasan Duniya nan, Lionel Messi ya tashi daga Barcelona, ya koma buga kwallo a kungiyar PSG da ke kasar Faransa.

Tauraron ‘dan wasa Lionel Messi ya hadu da tsohon kyaftin din Real Madrid, Sergio Ramos, wanda PSG ta dauko a kyauta a kakar wannan shekarar.

Jaridar AS ta kasar Sifen tace Sergio Ramos ya yi wa Lionel Messi kyakkyawar tarba, ya yi masa tayin su zauna tare a gidansa kafin ya samu matsuguni.

Kara karanta wannan

Kocin Barcelona ya bayyana ‘dan wasan da zai maye gurbin da Lionel Messi ya bari

Ya alakar Ramos da Messi ta ke?

Jaridar El País ta ce bayan sun hadu a birnin Faris, Ramos ya tuntubi Lionel Messi, ya na mai shaida masa a shirye yake da ya ba shi wurin zama a gidansa.

“Idan kai da iyalinka ku na sha’awar ku zauna a gida, maimakon otel, za ku iya zama a gida na."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sergio Ramos da Lionel Messi
Sergio Ramos da Lionel Messi Hoto: Hoto: CURTO DE LA TORRE (AFP)
Asali: UGC

El País ta ce PSG ta nema wa sabon ‘dan wasanta gidan da zai zauna, haka zalika makarantar da ‘ya ‘yansa uku; Thiago, Mateo da kuma Ciro za su yi karatu.

A lokacin da ake rade-radin Messi zai bar Barcelona, an rahoto Ramos yana cewa ‘dan wasan na Argentina zai iya zama a gidansa idan ya zabi ya je Madrid.

“Zai iya zama a nawa (gidan) na makon farko, ko yadda ta kama.”

Kara karanta wannan

Garkuwa da mutane: Ba a ga daman ceto yaran da ake sace wa bane inji Tsohon Ministan Buhari

“Zai ji dadin zama, ya saki jikinsa, zan ji dadi in yi masa wannan alfarma.”

Abokan gaba sun zama abokan wasa

A kasar Sifen, an shafe shekara da shekaru ba a ga maciji tsakanin Ramos da Messi, saboda gabar da ta ke tsakanin kungiyoyin Real Madrid da kuma Barcelona.

A karshe duka ‘yan wasan sun bar kungiyoyin da suka fi kauna. Messi ya yi shekara 17 ya na tare da Barcelona, Ramos ya shafe shekaru 16 kafin ya bar Madrid.

Ku na da labari cewa sai da wasu magoya bayan Barcelona suka kai korafi gaban hukumar kwallon kafa ta Turai da nufin a hana kungiyar PSG sayen Messi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng