Gwamna Zulum ya gana da Janar Irabor kan tubabbun 'yan Boko Haram

Gwamna Zulum ya gana da Janar Irabor kan tubabbun 'yan Boko Haram

  • A ranar Litinin, gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya ziyarci shugaban sojin kasa, Lucky Irabor a Abuja don tattaunawa akan tubabbun ‘yan Boko Haram
  • Sun yi ganawar da Zulum don nemo hanyar karyar guiwoyin manyan ‘yan ta’adda ta hanyar samar da jindadi ga tubabbun ‘yan ta’adda ta shirin ‘Operation Safe Corridor’
  • Anason samo hanyoyin da jama'a zasu karba tubabbun 'yan ta'addan ta yadda zasu shige cikin al'umma ba tare da banbanci ba

FCT, Abuja - A matsayin hanyar bullo wa tubabbun ‘yan Boko Haram daga bangarori daban-daban na jihar Borno, Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya kai ziyara Abuja wurin shugaban sojin kasa, Janar Lucky Irabor a ranar Litinin.

Za a yi taron sirrin ne don Zulum ya nemi sanin dabaru na shawo kan rashin tsaro a jihar Borno kuma masu fadi aji sune suka taso da batun samar da shirin ‘Operation Safe Corridor’ don tabbatar da jin dadi da walwala saboda karya guiwoyin sauran ‘yan ta’addan da basu tuba ba.

Kara karanta wannan

Yadda Janar Babangida ya taimakawa Goodluck Jonathan ya dare kan kujerar Shugaban kasa

Gwamna Zulum ya gana da Janar Irabor kan tubabbun 'yan Boko Haram
Gwamna Zulum ya gana da Janar Irabor kan tubabbun 'yan Boko Haram. Hoto daga prnigeria.com
Asali: UGC

Gwamna Zulum ya isa Abuja ne tun daga Maiduguri don yayi bincike iri-iri.

'Yan ta'addan Boko Haram suna ta mika wuya

Idan ba a manta ba, A ranar Asabar Zulum ta kai ziyara Bama da Gwoza don tattaunawa da shugabannin sojojin yankin da shugabannin garuruwan, prnigeria ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Anan ne ya bayyana shirin sa na z ama da shugaba Muhammadu Buhari, shugaban hukumar sojin kasa, sauran shugabannin tsaro, shugabannin addinai, manyan kasa, malaman addinai na kasa da jihohi da sauran manya wadanda suka fuskanci matsalolin rashin tsaro don lamarin ya tsananta.

Gwamnan ya kula da yadda dubannin ‘yan Boko Haram suka zubar da makamansu wanda hakan ya kawo karshen zubar da jinin da aka kai shekaru 12 ana yi, prnigeria ta ruwaito.

Sannan zasu tattauna akan hanyoyin samarwa da kwantarwa da mutane hankali akan tubabbun ‘yan ta’addan.

Kara karanta wannan

An sake ceto wata dalibar Chibok a jihar Borno, ta dawo da yara biyu

Hukumar NDLEA ta yi ram da wata mata ta boye sinki 100 na hodar iblis a filin jirgin Legas

Hukumar yaki da fasa-kwabrin miyagun kwayoyi, NDLEA tana cigaba da tabbatar da shirinta na kama masu safarar miyagun kwayoyi da kwace kwayoyin a hannunsu kamar yadda suka sanar.

A ranar Talata, 3 ga watan Augustan 2021 ne suka damke wata Mrs Nnadu Nora Chinyere, wata mai safarar miyagun kwayoyi tana kaisu kasar Italy, pR Nigeria ta ruwaito.

An kama ta ne a filin jirgin sama na Murtala Mohammed dake Ikeja, jihar Legas, dauke da nadi dari da kuma wasu dauri biyu na kwayoyin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: