Hukumar NDLEA ta yi ram da wata mata ta boye sinki 100 na hodar iblis a filin jirgin Legas
- NDLEA sun cigaba da tabbatar da tsarinsu na kama masu safarar miyagun kwayoyi da kwace kwayoyin a hannunsu
- Suna tsaka da kamen ne suka kama wata mata mai safarar miyagun kwayoyi tana kai su kasar Italy, Mrs Nnadu Chinyere
- An samu nasarar damkarta da miyagun kwayoyi dauri 100 da wasu kulli biyu a filin jirgin Murtala Mohammed dake Ikeja, jihar Legas
Legas - Hukumar yaki da fasa-kwabrin miyagun kwayoyi, NDLEA tana cigaba da tabbatar da shirinta na kama masu safarar miyagun kwayoyi da kwace kwayoyin a hannunsu kamar yadda suka sanar.
A ranar Talata, 3 ga watan Augustan 2021 ne suka damke wata Mrs Nnadu Nora Chinyere, wata mai safarar miyagun kwayoyi tana kaisu kasar Italy, pR Nigeria ta ruwaito.
An kama ta ne a filin jirgin sama na Murtala Mohammed dake Ikeja, jihar Legas, dauke da nadi dari da kuma wasu dauri biyu na kwayoyin.
Yadda aka kama matar
An kama ta ne yayin da ake bincike matafiyan Qatar Airways da zasu wuce Florentine, kasar Italy. An gano kwayoyin a cikin wasu robobin man wanke gashi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A ranar Alhamis, 12 ga watan Augustan 2021, jami’an MMIA suka kama wasu sunkin miyagun kwayoyi a NAHCO export na filin jirgin, pR Nigeria ta tabbatar.
Bayan an tsananta bincike, an ga 66.600kg na wiw, wiwi 1.600kg da hodar Iblis 1.450kg tare da wata da ta kai 69.65kg duk an boyesu a cikin kayan kwalliya.
An kama hodar Iblis da za a kai London
A ranar Alhamis, 5 ga watan Augustan wani jami’in filin jirgin ya kama wani kullin 25.8kg da aka boye a cikin kayan abinci za a kai London, UK duk a ma’adanar kaya na NAHCO export.
Kisan Gillan Musulmai a Jos: Kungiyar Kare Hakkin Musulmai MURIC Ta Yi Kira a Kame Kiristocin Irigwe
Bayan an bude kayan an duba su da kyau, an ga daurin hodar iblis, 2.3kg da sauran miyagun kwayoyi da aka dunkulesu da suka kai 23.5kg duk a ciki.
Da jami’an suna yawon kame a titin Akure-Owo sunci karo da wata mota a cikin Legas ta taso daga Owo zata Ibilo, jihar Kogi a ranar 7 ga watan Augusta.
A cikin motar an ga kulli 6 na miyagun kwayoyi 3.6kg; dauri 30 na hodar Iblis mai nauyin 87grams da ledojin Arizona mai nauyin 265grams.
Buba Marwa yayi jawabi
Shugaban hukumar NDLEA, Birgediya Janar Mohammed Buba Marwa mai murabus, ya yabawa jami’an filin jirgin MMIA da kuma takwarorinsu na Ondo, Borno, Binuwai da jihar Delta akan yadda suke amsar miyagun kwayoyi da kama masu safararsu.
Ya yaba musu kwarai kuma ya ce su cigaba da ayyukansu yadda ya dace, ya kuma bukaci sauran jami’an da su bi sahunsu, ya tabbatar musu da yadda shugaba Muhammadu Buhari yake ganin kokarinsu kuma yake yabawa.
Asali: Legit.ng