'Yan bindiga sun bude wa ma'aikatan da ke gina matatar man fetur wuta

'Yan bindiga sun bude wa ma'aikatan da ke gina matatar man fetur wuta

  • Rahoto daga jihar Imo na bayyana cewa, wasu 'yan bindiga sun hallaka wasu ma'aikatan matatar man fetur
  • An ce sun bude wa ma'aikatan wuta ne a kan hanyarsu ta zuwa wurin da ake aikin matatar mai
  • Rahoto ya ce, nan take mutane hudu suka mutu, yayin da wasu suka samu munanan raunuka

Imo - Akalla ma’aikatan kamfanin Injiniyanci na Lee hudu ne aka tabbatar sun mutu bayan da wasu ‘yan bindiga suka kai musu harin kwanton bauna da safiyar Litinin 16 ga watan Agusta a yankin Assa da ke karamar hukumar Ohaji/Egbema ta jihar Imo.

Wakilin jaridar Punch ya tattaro cewa ma’aikatan man suna kan hanyarsu ta wucewa zuwa wurin gina matatar mai a yankin Assa ne lokacin da ‘yan bindigan suka bude musu wuta.

Yayin da hudu suka mutu nan take, wasu sun samu munanan raunuka sakamakon harbin bindiga.

Kara karanta wannan

Sunayen Matafiya fiye da 20 da aka yi wa kisan gilla a Jos, wani ya rasa 'yanuwansa 7

Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun kai hari kan masu hakar danyen man fetur
Taswirar jihar Imo | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Wata majiya daga kauyen ta shaida cewa kamfanin na gina matatar mai ne a yankin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban Majalisar Matasan Ohaji na kasa, Emmanuel Ugorji, ya tabbatar da faruwar harin ga manema labarai.

Ya ce wasu shugabannin al'umma da jami'an tsaro, ciki har da shi, sun ziyarci wurin don ganewa idonsu.

Da yake yin kira ga gwamnati kan cewa ta karfafa tsaro a yankin, shugaban matasan ya ce 'yan bindigar na ta addabar yankin a cikin 'yan kwanakin nan.

Yadda jami'in tsaro ya harbi wata yarinya a garin warwason abinci a wurin biki

Bikin aure a Uyo, Jihar Akwa Ibom ya watse a ranar Asabar bayan da harsashin bindiga ya hallaka wata yarinya mai shekaru 15.

Lamarin ya biyo bayan harbi cikin kuskure da wani jami'in hukumar tsaro ta NSCDC da aka kawo don samar da tsaro a wurin taron ya yi.

Kara karanta wannan

Gada ta ruguje a Jigawa, ta hallaka matafiya ciki har da masu neman aikin soja

Wacce aka kashe, Veronica Kufre, tana karbar magani a sashin kulawa mai zurfi na wani asibiti mai zaman kansa a babban birnin jihar bayan asibitoci uku sun ki karbar ta.

An tattaro cewa lamarin ya faru ne a unguwar Nsukara, kusa da babban harabar jami'ar Uyo a lokacin da ake kokawar karbar abin sha da abinci a bikin.

An cafke mutane 20 cikin wadanda ake zargi da kisan musulmai a Jos

A baya, rundunar tsaro ta musamman, Operation Safe Haven (OPSH) a jihar Filato, ta cafke wasu mutane 12 da ake zargi da aikata kashe-kashe da safiyar Asabar a kan hanyar Rukuba ta karamar hukumar Jos ta Arewa a jihar, in ji rahoton PM News.

A sabbin rahotanni da suka shigo a yau kuwa, Daily Trust ta ruwaito cewa, mutane 20 ne ya zuwa yanzu a cafke da hannu wajen kisan musulmai 25 a wani yankin jihar Filato.

Kara karanta wannan

Yadda jami'in tsaro ya harbi wata yarinya a garin warwason abinci a wurin biki

Manjo Ishaku Takwa, jami’in yada labarai na rundunar, ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa ranar Asabar a garin Jos.

Asali: Legit.ng

Online view pixel