Da duminsa: Yan bindiga sun sake kai hari makaranta a Zamfara, sun kwashe dalibai, sun kashe yan sanda

Da duminsa: Yan bindiga sun sake kai hari makaranta a Zamfara, sun kwashe dalibai, sun kashe yan sanda

  • Yan bindiga na cigaba da cin karansu ba babbaka a Arewa maso yammacin Najeriya
  • Yayinda har yanzu akwai dimbin dalibai a hannunsu, sun sake kwashe wasu a Zamfara
  • Sun bukaci kudin fansar N350m kafin su saki daliban

Zamfara - Wasu yan bindiga sun hallaka jami'an tsaro, ciki har da dan sanda, a jihar Zamfara yayinda suka fasa kwalejin ilmin aikin noma dake karamar hukumar Bakura.

Yan bindigan sun yi awon gaba da dalibai da Malamai da yawa da har yanzu ba'a san adadinsu ba.

Rijistran makarantar, Aliyu Bakura, ya tabbatar da hakan ga BBC Hausa da safiyar Litinin.

Ya ce masu gadi uku da dan sanda 1 aka kashe.

A cewar jami'in makarantar, yan bindigan sun dira makarantar ne da muggan makamai

Da duminsa: Yan bindiga sun sake kai hari makaranta a Zamfara, sun kwace dalibai, sun kashe yan sanda
Da duminsa: Yan bindiga sun sake kai hari makaranta a Zamfara, sun kwace dalibai, sun kashe yan sanda
Asali: Original

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Barayin da Suka Sace Malamai, Dalibai a Kwalejin Zamfara Sun Nemi a Tattara Musu Miliyan N350m

Sun Nemi a Tattara Musu Miliyan N350m

Yan bindigan sun nemi a basu miliyan N350m kuɗin fansa kafin su sake daliban.

Da yake magana da Punch ta wayar salula, shugaban kwalejin, Alhaji Habibu Mainasara, yace barayin sun tuntuɓe shi ta wayar salula.

Yace yan bindiga sun nemi a ba su miliyan N350m kuɗin fansar mutum 20 dake hannun su a yanzun sannan su sako su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel