Katin gayyata: Jarumi kuma mawaki Garzali Miko zai angwance

Katin gayyata: Jarumi kuma mawaki Garzali Miko zai angwance

  • Shahararren jarumin masa'antar fina-finan Hausa kuma mawaki, Garzali Miko zai angwance a ranar Juma'a mai zuwa
  • Kamar yadda jarumin da sauran abokan sana'arsa suka dinga wallafa a shafukansu na Instagram, zai aura masoyiyarsa Habiba
  • Za a daura auren da karfe daya da rabi na rana a unguwar Rigasa dake garin Kaduna a masallacin Fajrul Islam

Kano - Fitaccen jarumin masana'antar Kannywood, gwanin rawa da waka, Garzali Miko ya shirya tsaf zai angwance da masoyiyarsa mai suna Habiba.

Kamar yadda jarumin tare da sauran abokan aikinsa suke ta wallafawa a shafukansu na Instagram, jarumi Garzali Miko zai aura masoyiyarsa ne a ranar Juma'a mai zuwa.

Katin gayyata: Jarumi kuma mawaki Garzali Miko zai angwance
Katin gayyata: Jarumi kuma mawaki Garzali Miko zai angwance. Hoto daga @garzalimiko
Asali: Instagram

Kamar yadda katin daurin auren ya bayyana, za a daura auren jarumi Garzali Miko da Habiba Umar Ahmda Dikwa da karfe 1 da rabi na ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

Ayiriri: Hoton Katin bikin Yusuf Muhammadu Buhari da Zahra Nasir Bayero ya bayyana

Za a daura ne garin Kaduna a anguwar Rigasa a cikin Masallacin Fajrul Islam.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Iyalan Mika'ilu Mai Lema da na Umar Ahmad Dikwa suna farin cikin gayyatarku zuwa wurin daurin auren 'ya'yansu:
Garzali Mika'ilu Mai Lema wanda aka fi sani da Garzali Miko da Habiba Umar Ahmad Dikwa wacce aka fi sani da Yarinya.

Za a yi shi kamar haka: Ranar Juma'a, ashirin ga watan Augusta da karfe daya da rabi na rana.
Wuri: Kaduna, layin Makarfi dake Rigasa a Masallacin Fajrul Islam.

Ayiriri: Hoton Katin bikin Yusuf Muhammadu Buhari da Zahra Nasir Bayero ya bayyana

Ana shirye-shiryen shagalin bikin auren dan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Yusuf Muhammadu Buhari da diyar Sarkin Bichi, Alhaji Nasir Ado Bayero, Gimbiya Zahra Nasir Bayero.

An fara bikin ne tun a makon da ya gabata inda aka fara da wasan Polo tare da wankan amarya, lamarin da ya janyo cece-kuce da maganganu daban-daban daga jama'a.

Kara karanta wannan

Bincike: Da gaske ne magajin Abba Kyari, Tunji Disu, sabon shugaban IRT ya isa ritaya?

Kwatsam a yau Juma'a, 13 ga watan Augusta, sai ga katin daurin ya bayyana inda @BBCHausa ta wallafa a shafinta na Instagram.

Kamar yadda katin ya nuna, za a yi daurin auren a ranar Juma'a, 20 ga watan Augusta wanda yayi daidai da 12 ga watan Muharram, shekara 1443 bayan hijirar Annabi Muhammadu S.A.W.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: