Ayiriri: Hoton Katin bikin Yusuf Muhammadu Buhari da Zahra Nasir Bayero ya bayyana

Ayiriri: Hoton Katin bikin Yusuf Muhammadu Buhari da Zahra Nasir Bayero ya bayyana

  • Tun a makon da ya gabata ne aka fara shirin auren dan shugaban kasa, Yusuf Muhammadu Buhari da Gimbiya Zahra Bayero
  • Katin daurin auren ya bayyana inda za a daura a ranar Juma'a, 20 ga watan Augusta, da karfe 1:30 na rana
  • Za a dauran auren soyayyan ne a fadar Sarkin Bichi, Alhaji Nasir Ado Bayero dake garin Bichi a jihar Kano

Bichi, Kano - Ana shirye-shiryen shagalin bikin auren dan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Yusuf Muhammadu Buhari da diyar Sarkin Bichi, Alhaji Nasir Ado Bayero, Gimbiya Zahra Nasir Bayero.

An fara bikin ne tun a makon da ya gabata inda aka fara da wasan Polo tare da wankan amarya, lamarin da ya janyo cece-kuce da maganganu daban-daban daga jama'a.

Ayiriri: Hoton Katin bikin Yusuf Muhammadu Buhari da Zahra Nasir Bayero ya bayyana
Ayiriri: Hoton Katin bikin Yusuf Muhammadu Buhari da Zahra Nasir Bayero ya bayyana. Hoto daga @BBChausa
Asali: Instagram

Kwatsam a yau Juma'a, 13 ga watan Augusta, sai ga katin daurin ya bayyana inda @BBCHausa ta wallafa a shafinta na Instagram.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Tsohon sakataren gwamnati, Alhaji Ahmad Joda, ya rasu

Bayanan da katin ya kunsa

Kamar yadda katin ya nuna, za a yi daurin auren a ranar Juma'a, 20 ga watan Augusta wanda yayi daidai da 12 ga watan Muharram, shekara 1443 bayan hijirar Annabi Muhammadu S.A.W.

A saman katin an fara saka tambarin kasa kafin daga bisani a zayyano sauran bayanai kamar haka:

Iyalan shugaban kasa Muhammadu Buhari, GCFR da na Mai Martaba, Alhaji Nasir Ado Bayero, Sarkin Bichi, suna farin cikin gayyarku zuwa wurin daurin auren dansu da 'yar su, Yusuf Muhammadu Buhari da Zahra Nasir Bayero.
Wanda aka shirya za a yi kamar haka:
Rana: 20 ga watan Augustan 2021, daidai da 12 ga watan Muharram, shekara 1443 bayan hijira.
Lokaci: Karfe 1:30 na rana Wuri: Fadar Sarkin Bichi, Bichi, jihar Kano.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Ana sa ran Shugaba Buhari zai dawo Najeriya a yau

Kotu ta dakatar da gwamnatin Kano daga gina shaguna a kan titunan Kantin Kwari

Wata babbar kotu a Kano da ta samu shugabancin Mai shari'a S. B Namallam ta dakatar da gwamnatin jihar Kano daga gina shaguna a kan titunan kasuwar Kantin Kwari.

A cikin kwanakin nan ne gwamnatin jihar Kano ta bada fulotai a tsakiyar layikan Ta'ambu da Bayajidda dake kasuwar Kantin Kwari, Daily Nigerian ta ruwaito.

Wannan al'amari babu shakka ya janyo cece-kuce tare da suka wanda jama'a suka dinga damuwa kan batun tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng