Bikin Sauya Sheka: Ministan Buhari Zai Koma Gida Jam'iyyar PDP

Bikin Sauya Sheka: Ministan Buhari Zai Koma Gida Jam'iyyar PDP

  • Shugaban PDP reshen jihar Ribas ya bayyana cewa nan gaba kaɗan Rotimi Amaechi zai koma PDP
  • Shugaban yace Amaechi ya koma APC ne domin kayar da shugaban kasa a wancan lokacin, Jonathan
  • A cewarsa tun da ya cika burinsa, to babu makawa zai koma asalin gidansa wato PDP

Rivers - Shugaban jam'iyyar PDP reshen jihar Ribas, Desmond Akawor, ya nuna yakinin cewa ministan sufuri, Rotimi Amaechi, zai koma PDP, kamar yadda punch ta ruwaito.

Akawor ya faɗi hakane a wurin wani taro a ƙaramar hukumar Ikwerre yayin da yake karbar masu sauya sheka daga wasu jam'iyyun siyasa zuwa PDP.

Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi
Bikin Sauya Sheka: Ministan Buhari Zai Koma Gida Jam'iyyar PDP Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Akawor yace:

"Yan uwanmu dake shigowa PDP, bara in faɗa muku wani abu, duk waɗannan shugabannin da kuke gani mambobin PDP ne, sun je can ne suga wainar da ake toyawa amma zasu dawo."

Kara karanta wannan

Abinda Shugaba Buhari Zai Fara Yi Bayan Dawowarsa Daga Landan, Femi Adesina

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Wata rana ministan sufuri, Chubuike Amaechi, ɗan mu ne, zai dawo gida jam'iyyar PDP. Inda ya koma, ya yi haka ne saboda wani dalili."

Wane dalili ya kai Amaechi APC?

Shugaban PDP na Ribas ya kara da cewa Amaechi ya koma APC ne kawai domin yaga an kwace mulki daga hannun tsohon shugaba, Jonathan.

Akawor ya kara da cewa:

"Ya koma can ne yaga bayan shugaba Jonathan kuma burin shi ya cika don haka zai dawo gida PDP. Na faɗi haka amma ance kada na maimaita."
"Amma yanzun nan a Ikwerre zan sake faɗa. Ɗan uwana, Abokina, babban abokin gwamnan mu Nyesom Wike, Rotimi Amaechi, kadawo gida PDP."

Shugaban PDP ya yaba wa Wike

Tun da farko, shugaban PDP na karamar hukumar Ikwerre, ya yabawa gwamna Nyesom Wike da sauran shugabannin PDP na kasa da suka ceto jam'iyyar daga rugujewa.

Kara karanta wannan

Dan Arewa kadai zai iya ciwa PDP zaben shugaban kasa a 2023, Mai gidan talabijin na AIT

A jawabinsa yace:

"Muna mika godiya ga gwamnan mu da sauran shugabannin PDP a Najeriya bisa warware matsalar da ta kusa rushe mu watannin da suka gabata."

A wani labarin kuma Bikin Sauya Sheka, Gwamnonin Jam'iyyar APC Sun Shiga Ganawar Sirri da Wani Tsohon Gwamna

Tsohon gwamnan jihar Oyo, Rashidi Ladoja, ya gana da gwamnonin jam'iyyar APC uku a Ibadan.

Taron wanda aka shafe sama da awanni uku ana yinsa ya gudana ne a gidan Ladoja dake Ibadan, babban Birnin Oyo.

Duk da cewa babu wani cikakken bayani game da abinda suka tattauna, amma ana tsammanin ganawar tana da alaƙa da sauya sheka zuwa APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel