An sheke mutum 5, wasu 5 sun jigata a sabon harin da miyagu suka kai kudancin Kaduna

An sheke mutum 5, wasu 5 sun jigata a sabon harin da miyagu suka kai kudancin Kaduna

  • Miyagun 'yan bindiga sun kai farmaki kauyen Madamai dake karamar hukumar Kaura ta jihar Kaduna
  • An gano cewa sun tsinkayi kauyen wurin karfe 5 na asuban Lahadi inda suka dinga harbe-harbe babu kakkautawa
  • Sun sheke mutum 5, 5 sun jikata yayin da suka kone gidaje 9, ababen hawa 3 duk a cikin kauyen dake jihar Kaduna

Kaduna - A kalla mutane biyar ne suka sheka lahira yayin da wasu biyar suka jigata sakamakon farmakin da miyagu suka kai yankin Madamai dake karamar hukumar Kaura ta jihar Kaduna a ranar Lahadi, Daily Trust ta ruwaito.

Wani ganau ba jiyau ba wanda ya tsallake farmakin da harbin bindiga mai suna Emmanuel Nache, ya sanar da Daily Trust cewa maharan sun kutsa yankin da yawansu wurin karfe biyar na asuba kuma sun dinga harbe-harbe.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Kai Hari Kauyuka Sun Kashe Mutane da Dama Tare da Sace Wasu a Sokoto

An sheke mutum 5, wasu 5 sun jigata a sabon harin da miyagu suka kai kudancin Kaduna
An sheke mutum 5, wasu 5 sun jigata a sabon harin da miyagu suka kai kudancin Kaduna. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Ganau ya bada labari dalla-dalla

Yayin da naje gona da sassafe, na fara jin harbin bindiga kuma a lokacin da na fara gudu ne harsashi ya same ni a hannun dama, yace.

Nache mai shekaru hamsin da shida ya kara da cewa maharan sun tarwatsa gidaje da gonakin yankin.

Wata Linda Moses mai shekaru talatin da daya wacce ta sha da kyar, tace ta gano gawawwakin mutum hudu da 'yan bindigan suka kashe a yankin.

An harba diyar Linda mai suna Joyce Moses mai shekaru 12 kuma 'yar aji biyar a firamare a gabanta. Mutum biyar sun jigata kuma suna karbar taimakon likitoci a asibitin Kashim Ibrahim Yakowa dake Kafanchan.

A ina kauyen Madamai yake?

Madamai kauye ne dake karamar hukumar Kaura ta jihar Kaduna wanda ke da iyaka da Jankasa dake karamar hukumar Zangon Kataf a jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Gurneti ya tashi da kananan yara 5 a Ngala, jihar Borno

A yayin tabbatar da aukuwar lamarin, kwamishinan tsaron cikin gida, samuel Aruwan, yace an sheke mutum biyar, an kone gidaje 9, ababen hawa 3 yayin da maharan suka tsinkayi kauyen.

Wadanda suka rasa rayukansu kamar yadda Aruwan ya tabbatar sune: Janet Yakubu, Gambk Yakubu, Jonathan Adamu, Mrs Monday da Humphrey Barnabas.

Mukaddashin gwamnan jihar Kaduna, Hajiya Hadiza Sabuwa Balarabe ta roki jama'ar yankin da su kwantar da hankalinsu yayin ta umarci jami'an tsaro da su gaggauta bincikar lamarin,"Takardar ta kara da cewa.

Mummunar Gobara ta yi wa Gidan Talabijin Kurmus a Jihar Ogun

Wata kazamar gobara ta kone gidan talabijin din Hi-Impact, gidan watsa shirye-shiryen talabijin na HD na farko a Najeriya dake jihar Ogun.

Bangaren watsa shirye-shiryen yana harabar Hi-Impact Planet Amusements Park & Resort dake wurin kilomita 12 a titin Lagos zuwa Ibadan a Ibafo dake karamar hukumar Obafemi Owode jihar Ogun.

Kara karanta wannan

Da gwamnati ta biya kudin fansata, ana sako ni zan yi murabus, Kwamishinan Niger

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel