Mummunar Gobara ta yi wa Gidan Talabijin Kurmus a Jihar Ogun

Mummunar Gobara ta yi wa Gidan Talabijin Kurmus a Jihar Ogun

  • Wata kazamar gobara ta lashe gidan talabijin din Hi-Impact, gidan watsa labarai na HD na farko a Najeriya
  • Gobarar ta fara cin ma’aikatar ne a ranar Alhamis sannan wurin watsa shirye-shiryenta ya kone kurmus
  • Hukumar kashe gobarar jihar Ogun ne ta tabbatar da aukuwar lamarin a wata takarda ta ranar Juma’a

Ogun - Wata kazamar gobara ta kone gidan talabijin din Hi-Impact, gidan watsa shirye-shiryen talabijin na HD na farko a Najeriya dake jihar Ogun.

Bangaren watsa shirye-shiryen yana harabar Hi-Impact Planet Amusements Park & Resort dake wurin kilomita 12 a titin Lagos zuwa Ibadan a Ibafo dake karamar hukumar Obafemi Owode jihar Ogun.

Mummunar Gobara ta yi wa Gidan Talabijin Kurmus a Jihar Ogun
Mummunar Gobara ta yi wa Gidan Talabijin Kurmus a Jihar Ogun. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Daily Trust ta ruwaito cewa, gobarar ta fara ne tun ranar Alhamis kuma bangaren watsa shirye-shiryen ya cinye kone kurmus.

Kara karanta wannan

Dalibar aji 1 a sakandire ta maka gwamnatin Ekiti a kotu, tana bukatar diyyar N15m

Hukumar kwana-kwana ta tabbatar da aukuwar lamarin

Hukumar kwana-kwanan jihar Ogun ne ta tabbatar da aukuwar lamarin a wata takardar da suka saki a ranar Juma’a.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda takardar wacce jami’in hulda da jama’an hukumar kwana-kwanan, Bunkunola Kuti, ya sanya hannu, ya ce an gano tushen gobarar kuma cikin hanzari ma’aikatan kwana-kwanan suka kashe wutar.

Kamar yadda takardar tazo:

Jami’an kwana-kwana dake Isheri a jihar Ogun wacce Injiniya Akinwande Abiodun yake shugabanta, sun amsa kiran da ma’aikatar yada labarai tayi.

Sannan sun tabbatar da cewa babu asarar rai ko daya, sai dai duk wasu tsadaddun kaya sun kone a wurin, Daily Trust ta wallafa.

Kwanishinan harkoki na musamman, Barista Femi Ogunbanwo da darektan hukumar kwana-kwanan jihar, Fatai Adefala ya kai ziyara a maimakon gwamnati kuma ya jajanta wa kamfanin da ma’aikatan akan mummunan al’amarin.

Kara karanta wannan

Ku cire ni daga rikicin shugabancin APC – Tsohon Shugaban jam’iyyar Oshiomhole

Farar shinkafa babu miya ake bamu sau 1 a rana, Wadanda suka kubuta daga hannun miyagu

Halima Falalu-Umar mai shekaru 10, ta tsere daga hannun masu garkuwa da mutane a sansaninsu dake Kaduna ta bayyana yadda masu garkuwa da mutane suka yi ta basu farar shinkafa babu miya sau daya a rana tun da suka sacesu.

Halima ta samu ta tsere tare da ‘yan uwanta; Bashir Nura-Umar da Khadija Falalu-Umar mai shekaru 7, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel