An damke Hadimin tsohon Shugaban kasa Jonathan da laifin alfasha a kasar waje

An damke Hadimin tsohon Shugaban kasa Jonathan da laifin alfasha a kasar waje

  • Ana jita-jitar an cafke Kingsley Kuku a babban filin jirgin kasar Netherlands
  • Kingsley Kuku ya shiga hannu ne bisa zarginsa da yada wata alfasaha a 2018
  • Kuku ya na cikin masu ba Shugaban Najeriya shawara daga 2011 zuwa 2015

Amsterdam - Kingsley Kuku, wanda ya rike kujerar Mai ba shugaban kasa shawara a lokacin da Goodluck Jonathan yake mulki, ya shiga hannun hukuma.

Kuka ya fada hannun hukumomin waje

Rahotanni daga SaharaReporters sun ce an damke Kingsley Kuku ne a Amsterdam, kasar Netherlands.

Ana zargin cewa an kai karar Kuku da laifin yada alfasha ne na wani wanda bai balaga, hakan ya sa aka yi ram da shi a hanyar zuwa Ingila daga Amsterdam.

Politics Nigeria ta ce an kama wannan mutum mai shekara 51 a babban filin jirgi na Amsterdam Schiphol, ya na mai shirin zuwa birnin Landan, Birtaniya.

Kara karanta wannan

Sanusi II: Najeriya ba ta cimma komai ba cikin shekaru 40, dole na fadi gaskiya

Kamar yadda rahoton ya bayyana a jiya, hukumomi sun dade suna neman Kuku a Schiphol, sai yanzu ne da yake zuwa daga Ghana, aka samu aka kama shi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"An kama Kingsley Kuku ne a birnin Amsterdam.”

Kingsley Kuku Hoto: www.today.ng
Hon. Kingsley Kuku Hoto: www.today.ng
Asali: UGC

“An bada umarnin a cafke shi ne saboda zargin yada alfashar karamin yaro. An kama shi kwanaki hudu (yanzu biyar kenan) da suka wuce.”

Tsohon ‘dan majalisar dokokin na jihar Ondo ya yada wasu alfasha tun a shekarar 2018, bayan mai gidansa ya bar kan mulki, sai a yanzu ne ya shigo hannu.

Hon. Kingsley Kuku ya yi aiki da Goodluck Jonathan

A lokacin da Jonathan yake mulkin Najeriya, Kuku ya kasance hadimin da yake taimaka masa a kan harkokin Neja-Delta, ya jagoranci shirin sulhu da ake yi.

A farkon 2011 Kuku ya zama shugaban tsarin Niger Delta Presidential Amnesty Programme da aka shigo da shi domin inganta rayuwar tsagerun Neja-Delta.

Kara karanta wannan

Karin haske: An cafke mutane 20 cikin wadanda ake zargi da kisan musulmai a Jos

Jaridar The Will ta ce an zargi Kuku da karkatar da biliyoyin kudi daga wannan zargi a lokacin da yake ofis, har aka kafa wani kamfanin jiragen sama a Najeriya.

Doyin Okupe ya dage a kan batun 2023

A baya an ji wani tsohon hadimin shugaban kasa, Dr. Doyin Okupe ya na cewa shi ya fi dace wa da ya dare a kan kujerar shugaban Najeriya a zaben da za ayi a 2023.

Doyin Okupe ya ce shi da Osinbajo suka cika sharudan da Janar Ibrahim Babangida ya sa na wanda zai zama shugaban kasar nan domin ya zagaye Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel