Matasan mayakan Boko Haram 14, mata da yara 31 sun sake mika wuya a Konduga

Matasan mayakan Boko Haram 14, mata da yara 31 sun sake mika wuya a Konduga

  • Karin yan Boko Haram 45 sun mika wuya ga Sojoji ranar Litinin
  • Sun bayyana dalilin da yasa suka yanke shawarar ajiye makamansu
  • Wannan shine karo na uku da yan ta'adda zasu mika wuya kwanan nan

Akalla mutum 45 wanda ya hada da mayakan Boko Haram/ISWAP matasa yan kasa da shekaru ashirin guda 14 tare da mata da yara 31 sun mika wuya ga Sojoji a ranar Litinin.

An tattaro cewa tubabbun yan ta'addan sun alanta fitarsu daga Boko Haram ne a karamar hukumar Konduga ta jihar Borno, Arewa maso gabashin Najeriya.

Sun mika kansu ne ga kwamandojin rundunar Operation Hadin Kai.

PRNigeria ta ce a cewar wani jami'in leken asiri na hukumar Soji wanda ya bukaci sakaye sunansa, wannan karon yan ta'addan basu mika wuya tare da makamansu ba.

Yace:

"Daga cikin yan ta'adda 45 da suka mika wuya, 21 sun fito ne daga Garin Dinya, kuma 22 daga kauyen Jaja Kalwa."

Kara karanta wannan

Ku Tuba Ku Mika Makamanku Tun Kafin Mu Karaso, COAS Yahaya Ga Yan Ta'adda

mayakan Boko Haram 14, mata da yara 31 sun sake mika wuya a Konduga
Matasan mayakan Boko Haram 14, mata da yara 31 sun sake mika wuya a Konduga Hoto: prnigeria.com
Asali: UGC

Mutum biyar daga cikin yan ta'addan sun bayyanawa PRNigeria cewa an tilastasu shiga kungiyar yan ta'adda ne.

Modi Malaram daga Jaja Kalwa yace:

"Wallahi, yawancinmu yara ne kuma marasa karfi na yakan kwamandojin Boko Haram da suka sacemu daga kauyukanmu."
"Tun a baya mun san kungiyar na shaidnu ne, amma mun kasa yaki da su saboda kashemu za'a yi. Wadanda sukayi kokarin guduwa a gabanmu aka kashesu."
"Duk da ni da iyalina mun mika wuya, ban tunanin mutan garinmu zasu sake yarda da mu."

Akwai rabuwar kai tsakanin kwamandojin Boko Haram

Malaram ya kara da cewa yanzu haka akwai rabuwar kai tsakanin kwamandojin kuma haka ya sa suka iya fitowa mika wuya.

"Bayan mutuwar Shekau, an samu sabanin cikin gida da fadace-fadace, kuma hakan ya faranta mana rai. Amma kuma ruwan wutan da sojoji keyi ya tilasta mana guduwa da sansaninsu. Haka yasa muka fito don mika wuya," ya kara.

Kara karanta wannan

'Yan Boko Haram 605 sun mika wuya ga sojoji, yunwa da annoba sun dira sansaninsu

An samar wa sojojin da ke yakar 'yan Boko Haram jirgin yawo lokacin hutu

A bangare guda, rundunar Sojin Najeriya ta bayyana cewa za a samar da jirgin saman zirga-zirga ga sojoji da manyan jami'ai a fagen daga wadanda aka ba izinin ficewa na wucin gadi da nufin zuwa ganin danginsu yayin da suke kan aiki.

Jaridar TheCable ta ba da rahoton cewa izinin ficewar, a yaren sojoji, izini ne na barin sashin aiki na dan wani lokaci.

Legit.ng ta tattaro cewa mafi yawan sojoji da jami'ai da aka tura daga sassa daban-daban na kasar zuwa rundunar Operation Hadin Kai a arewa maso gabas suna tafiya daruruwan kilomita lokacin da suke kan izinin ficewa na wucin gadi domin ganin danginsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel