Mala Buni da Jam’iyyar APC sun samu tulin korafi daga jihohi 14 a sakamakon zaben shugabanni

Mala Buni da Jam’iyyar APC sun samu tulin korafi daga jihohi 14 a sakamakon zaben shugabanni

  • Jam’iyyar APC ta samu korafe-korafe daga zabukan mazabu da aka gudanar
  • Mai Mala Buni ya kafa kwamitocin da za su saurari karar da aka kai gabansa
  • Wannan zai jawo karin bata lokaci wajen shirya zabukan kananan hukumomi

An samu korafe-korafe a sakamakon zabukan shugabanni da jam’iyyar APC mai mulki ta gudanar kwanaki a mazabun da ke jihohin fadin kasar nan.

Jaridar The Nation ta ce jam’iyyar APC ta samu korafi daga jihohi akalla 14, inda wasu ‘ya ‘yan jam’iyyar suka kai kararsu gaban kwamitin rikon kwarya.

Rahoton ya ce jihohi 12 ba su gabatar da rahoton zabukan da aka yi ga kwamitin Mai Mala Buni ba.

Ana tunanin cewa idan ba a kammala maganar zabukan mazabu ba, ba za a sa ranar da za a gudanar da zaben shugabanni na kananan hukumomi ba.

Kara karanta wannan

Neman a tsige Buni daga kujerar gwamna: APC ta yi wa PDP wankin babban bargo

Jam’iyyar APC ta kafa wasu kwamitoci da za su saurari korafin da aka gabatar. An rantsar da wadannan kwamitoci ne a ranar 12 ga watan Agusta, 2021.

Shugaban APC na rikon kwarya, Mai Mala Buni, ya rantsar da wadannan kwamitoci masu dauke da mutane biyar a sakatariyar APC a birnin tarayya, Abuja.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mala Buni da Jam’iyyar APC sun samu tulin korafi daga jihohi 14 a sakamakon zaben shugabanni
Mai Mala Buni da Shugaban kasa @APCNigeria
Asali: Facebook

Rantsar da wadannan kwamitoci da za su sasanta fusatattun ‘yan jam’iyyar ya zo ne bayan kwana biyar da ya kamata a ce an karkare batun zabukan.

An shirya zaben shugabannin mazabun na APC ne makonni biyu da suka wuce, amma har yanzu ba a kai ga gudanar da ragowar zabukan da za su biyo ba.

A jihohin Anambra, Bayelsa da Zamfara ne kadai jam’iyyar APC ba ta yi zabukan ba saboda wasu dalilai.

Majiyar ta ce jihohin da aka samu korafi sun hada da Akwa Ibom, Enugu, Neja, da Kwara. Ragowar jihohin da aka samu sabanin su ne Ekiti, Osun da kuma Kano.

Kara karanta wannan

Fusatattun ‘Ya ‘yan Jam’iyya sun yi bore, sun maka Buni da shugabannin APC a gaban kotu

Progressives Consolidation Group ta na tare da Osinbajo

Magoya-baya sun fara yi wa Yemi Osinbajo yakin zama Shugaban kasa a zaben 2023 a APC.

Kungiyar Progressives Consolidation Group ta aika wa wasu manyan jam'iyyar APC wasika, ta na tallata takarar Osinbajo a zabe mai zuwa domin ya canji Buhari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel