Kungiya ta rubutawa Gwamnoni, ‘Yan Majalisa takarda, tace Osinbajo ya dace ya gaji Buhari
- Kungiyar Progressives Consolidation Group tana goyon bayan Yemi Osinbajo
- PCG ta ce Farfesa Osinbajo ne ya kamata ya canji Muhammadu Buhari a 2023
- Shugabannin PCG sun rubuta wasika, suna neman goyon bayan manyan APC
Abuja - Kungiyar Progressives Consolidation Group ta aika wa shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan da wasu ‘yan APC takarda game da shirin 2023.
2023: Kungiyar PCG ta bayyana 'dan takararta
Kungiyar PCG tayi kira ga Sanata Ahmad Lawan da sauran wadanda jam’iyyar APC ta ke ji da su, da su goyi bayan takarar Farfesa Yemi Osinbajo a zaben 2023.
Jaridar Daily Trust ta samu labarin cewa wannan wasika mai shafi uku ta yi kira ga gwamnonin APC, Sanatoci da ‘yan majalisar wakilai su mara wa tafiyar baya.
Wannan kungiya ta aika wannan wasika mai taken "APC and the future of Nigeria: Why we must get it right & consider the Osinbajo option in 2023″ a ranar Alhamis.
Shugaban PCG da sakatarensa na kasa Alhaji Ahmed Mohammed da Dr. Eberechukwu Eli Dibia sun sa hannu a wasikar, suna kira a ba Osinbajo dama ya yi takara.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Bangaren wasikar PCG
“Mai girma, muna rubuta maka wannnan takarda ne a matsayinka na shugaban majalisar dattawa, daya daga cikin manyan jam’iyyar mu ta kowane bangare, ka na cikin wanda Ubangiji ya daukaka da nauyi a tarihin Najeriya.”
“Mu ‘ya kungiyar Progressive Consolidation Group (PCG), muna neman goyon bayanka, ka mara mana baya wajen kiran da mu ke yi na ayi la’akari da Osinbajo a matsayin magajin wanda zai gaji Muhammadu Buhari, GCFR a 2023."
“Mun yi amanna ba tare da kokwanto ba cewa, samun mataimakin shugaban kasa, Osinbajo ya karbi ragamar mulki, zai taimaka wa tafiyar da ake kai.”
Ahmed Mohammed da Dr. Eli Dibia suka ce idan Farfesa Yemi Osinbajo ya samu madafan iko, babu tantama kasa za ta ga cigaba, tare da samun zaman lafiya.
Zuwa yanzu da irin wannan kungiya suka zake, Farfesa Osinbajo bai bayyana niyyar takara ba.
Bode George ya na adawa da Tinubu
A makon nan ne aka ji babban jigon PDP, Cif Bode George ya na cewa ya kamata a duba kwakwalwar duk wani mai goyon bayan Bola Tinubu a 2023.
Bode George ya ce har gobe Tinubu ya na amfani da kamfaninsa, ya na tatsar arzikin Legas. 'Dan siyasar ya ce jagoran na APC bai da shaidar zuwa makaranta.
Asali: Legit.ng