Fusatattun ‘Ya ‘yan Jam’iyya sun yi bore, sun maka Mala Buni da shugabannin APC a gaban kotu

Fusatattun ‘Ya ‘yan Jam’iyya sun yi bore, sun maka Mala Buni da shugabannin APC a gaban kotu

  • An samu wadanda suka shigar da karar jam’iyyar a kotu a jihar Ondo
  • Segun Boboyi da kuma Idowu Adebusuyi ne suka kai jam’iyyarsu kotu
  • Adebusuyi yace rashin adalcin APC ya jawo suka dauki hayar Lauyoyi

Ondo - Wasu daga cikin fusatattun ‘ya ‘yan jam’iyyar APC a karamar hukumar Ifedore, jihar Ondo, sun shigar da karar jam’iyya a wani kotu da ke zama a Akure.

Jaridar Punch ta ce ‘ya ‘yan APC mai mulkin suna neman Alkali ya soke zabukan shugabannin mazabu da jam’iyyar APC ta shirya a cikin ‘yan kwanakin nan.

Su wanene suka kai jam’iyyarsu kotu?

Rahoton ya ce wadanda suka shigar da karar wasu jagororin APC ne; Segun Boboyi da Idowu Adebusuyi.

Daga cikin wadanda za su kare kansu a gaban Alkali akwai shugaban APC na rikon kwarya, Mai Mala Buni, Gboyega Isiaka, Ade Adetimehin, da Tunde Fawoyi.

Haka zalika lauyoyin Boboyi da Adebusuyi sun hada da hukumar INEC a cikin wannan shari’ar.

Kara karanta wannan

Rikicin cikin gidan PDP ya kara kamari, Mataimakan Secondus sun juya masa baya

Buhari & Rotimi Akeredolu
Muhammadu Buhari da Rotimi Akeredolu na Ondo Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Lauyoyin da suka shigar da kara suna so kotu ta yi watsi da hukuncin da wadanda ake kara suka dauka wajen gudanar da zabuka a mazabun da ke Ifedore.

Ana neman Alkali ya bada damar soke zabukan da sunan cewa zaben shugabannin bai halatta ba, domin ba a bi dokar kasa ba, sannan an saba wa tsarin mulki.

Meya sa aka kai jam’iyyar APC kara a kotu?

Da yake magana a ranar Talata, 10 ga watan Agusta, 2021, game da abin da ya sa suka je kotu, Idowu Adebusuyi ya bayyana cewa APC ba ta yi masu adalci ba.

A cewar Idowu Adebusuyi, ba a tafi da mafi yawan ‘yan jam’iyyar APC na karamar hukumar Ifedore wajen yin fito da shugabanni ba, don haka suka ja daga.

Jigon na APC ya ce shugaban majalisar dokoki na Ondo, Rt. Hon. Bamidele Oloyeloogun, ya na goyon bayansu, kuma shugabannin jam’iyya sun san da karar.

Kara karanta wannan

Kotu ta ce a karbe kadarori fiye da 500 da tsohon Gwamnan APC ya mallaka lokacin ya na ofis

Za a binciki Shugaban APC a Yola

A gefe guda kuma an ji cewa shugaban Jam’iyyar APC na Yola ta kudu da yake addu’a COVID-19 ta kashe shugaban kasa Muhammadu Buhari zai fuskanci kwamiti.

Jam’iyya ta kafa kwamiti da zai binciki shugabanta da aka ji ya na baram-barama a wajen wani taro na masu ruwa da tsaki da aka shirya kwanaki a jihar Adamawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng