Indonisiya ta yi nadama kan yadda aka ci zarafin jami'in diflomasiyyar Najeriya

Indonisiya ta yi nadama kan yadda aka ci zarafin jami'in diflomasiyyar Najeriya

  • Gwamnatin kasar Indonisiya ta bayyana nadamar yadda aka makure wani jami'in Najeriya
  • Rahotanni sun bayyana yadda wasu jami'an kasar Indonisiya sun makure wani dan Najeriya
  • Lamarin ya faru ne a ranar 7 ga watan Agusta, kuma batun ya jawo cece-kuce a Najeriya

Gwamnatin Indonisiya ta bayyana yin nadama da abin da ya faru da jami’in diflomasiyar Najeriya inda wani bidiyo a shafukan sada zumunta ya nuna jami’anta na shige da fice sun makure shi, BBC Hausa ta ruwaito.

Bidiyon ya nuna yadda jami’in mai suna Abdulrahman Ibrahim wasu maza sun cukuikuye shi a cikin mota.

Najeriya bayan fitar bidiyon ta nuna fushinta tare da yin Allah wadai da abin da ya faru wanda ta ce “ya saba dokar kasa da kasa.”

Indonisiya ta yi nadama kan yadda aka ci zarafin jami'in diflomasiyyar Najeriya
Jakadan Najeriya da aka makure | Hoto: bbc.com/hausa
Asali: UGC

Sanarwar da ma’aikatar harakokin wajen Indonisiya ta fitar ta ce abin da ya faru ranar 7 ga Agusta 2021 wani abu ne na daban kuma ba zai sauya huldarta da ba da dakatar da ayyukanta na kula da jami’an diflomasiya ba.

Kara karanta wannan

Twitter ta yi martani bayan gwamnati ta sanar da dage dokar haramtata a Najeriya

FG ta kira jakadan Najeriya, tayi barazanar sake duba alakarta da Indonisiya bayan cin zarafin jami’inta

Gwamnatin tarayya ta yi barazanar sake duba alakarta da Indonesiya bayan harin da jami’an shige da fice na kasar suka kaiwa jami’in diflomasiyyar Najeriya.

Ministan harkokin kasashen waje, Geoffrey Onyeama, ya bayyana hakan a wani taro da aka gudanar a Abuja a ranar Talata, 10 ga watan Agusta.

Onyeama ya kuma ce an gayyaci jakadan Najeriya a Indonisiya don ci gaba da tuntuba da kuma bayar da cikakken bayani kan harin.

Legit.ng ta bayyana cewa takaitaccen bayanin Onyeama ya biyo bayan la'antar da ma'aikatar ta yi a baya game da harin wanda aka nada a wani bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: FG ta kira jakadan Najeriya, tayi barazanar sake duba alakarta da Indonisiya bayan cin zarafin jami’inta

Twitter ta yi martani bayan gwamnati ta sanar da dage dokar haramtata a Najeriya

A wani labarin, Gwamnatin tarayya, ta hanyar ministan yada labarai da al'adu, Lai Mohammed ta sanar da dage dokar hana Twitter, kana kamfanin zai bude ofishinsa a Najeriya.

Mohammed ya bayyana haka ne a ranar Laraba, 11 ga watan Agusta, yayin da yake zantawa da wakilan gidan gwamnati bayan kammala taron majalisar zartarwa ta tarayya a Abuja.

Ministan ya ce ya zuwa yanzu, gwamnati ta dage dakatar da shafin tare da wasu sharudda wadanda wasu daga ciki sun hada da yin rijista da Hukumar Harkokin Kasuwanci (CAC).

Jaridar Punch ta bayyana cewa wasu sharuddan sune tilastawa Twitter daukar wakili dan kasa, yin rajista tare da kungiyoyi kamar NIPDA, kamar NCC, NBC, da jajircewar yin aiki tare da Ma'aikatar Haraji ta Tarayya don biyan haraji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel