Amurka ta bukaci gaggauta garkame Abba Kyari cikin Kurkuku kafin ya gurfana a kotu

Amurka ta bukaci gaggauta garkame Abba Kyari cikin Kurkuku kafin ya gurfana a kotu

  • Har yanzu ana samun sabbin bayanai kan zargi da ake yiwa Abba Kyari
  • Hukumar yan sandan Najeriya ta dakatar da shi dommin gudanar da bincike
  • Abba Kyari yace yana da gaskiyarsa kuma zata bayyana\

Kasar Amurka ta bukaci a garkame jami'in dan sandan da aka dakatar, DCP Abba Kyari, kafin gurfanar da shi a kotu, wasu takardun birnin California a Amurka suka nuna. '

Thisday ta ce ta samu ganin wadannan takardu na kotu.

Takardun kotun masu dauke da ranar wata 29 ga Afrilu, 2021, da kuma sa hannun mukaddashin Antoni na Amurka, Tracy Wilkinson ya bukaci garkame Kyari.

Takardar tace:

" Mai kara, Amurka na bukatar garkame abin zargin (Abba Kyari) saboda wadannan dalilai:
"Garkame mutum kafin ya gurfana a kotu saboda babu hujjan cewa:
a. Wanda ake tuhuman zai bayyana a kotu
b. Kare rayukan sauran jama'an gari."

Amurka ta kara da cewa takardun kotun gwamnati na da hakkin garkameshi bisa sashe na S 3142 (f) idan akwai tsoron wanda ake tuhuma zai iya guduwa.

Kara karanta wannan

Gaskiya za ta bayyana, kowa ya san bana karya: Abba Kyari ya sake jaddadawa

Amurka ta bukaci garkame Abba Kyari cikin Kurkuku kafin ya gurfana a kotu
Amurka ta bukaci gaggauta garkame Abba Kyari cikin Kurkuku kafin ya gurfana a kotu Hoto: Abba Kyari

Gaskiya za ta bayyana, kowa ya san bana karya: Abba Kyari ya sake jaddadawa

Abba Kyari ya jaddada cewa shi fa yana da gaskiya kan tuhumar da ake masa kuma nan ba da dadewa ba gaskiya zai bayyana.

Abba Kyari ya bayyana hakan ne a jawabin da ya daura a shafin yanar gizon tsaffin wadanda suka halarci wani taro a Amurka.

Yace dukkan abubuwan da ya fada kuma ya daura a shafinsa gaskiya ne.

Yace:

"Dukkan wadanda suka san ni sosai sun san ba na son karya. Dukkan abinda na fada ko na wallafa gaskiya ne. Nan ba da dadewa ba gaskiyar lamarin nan zata bayyana."

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

iiq_pixel