Yan Sanda Sun Kwace Iko da Sakateriyar APC Yayin da Mambobin Kwamitin Zartarwa Suka Tsige Shugaban APC
- Rikicin APC a jihar Enugu ya ɗauki wani sabon salo ranar Laraba yayin da jami'an yan sanda suka kwace sakateriya
- Babu wani mamba ko jigon jam'iyyar da jami'an sanda suka bari ya shiga ofishin yayin da suke kokarin dawo da doka da oda
- Jam'iyyar ta tsige shugabanta na jihar inda ake zarginshi da zagon kasa da kuma fatali da dokoki
Enugu - Jami'an hukumar yan sanda sun kwace iko da ofishin jam'iyyar All Progressive Congress (APC) a jihar Enugu domin dawo da doka da oda.
PM News ta ruwaito cewa jami'an sun hana shugabannin jam'iyyar da sauran masu faɗa aji shiga ofishin biyo bayan rikicin shugabanci da ya ɓarke a APC reshen jihar.
Mambobin SEC sun tsige shugaban APC
Legit.ng ta ruwaito cewa mambobin kwamitin zartarwa na jam'iyyar APC reshen jihar Enugu sun amince da tsige shugabansu, Dr Ben Nwoye, bayan kaɗa kuri'a.
Kwamitin ya zargi tsohon shugaban Nwoye da rashin ɗa'a da kuma kawo hargitsi da rabuwar kai a cikin jam'iyyar APC.
Kwamitin ya shaidawa manema labarai cewa sun ɗauki wannan matakin ne saboda zagon kasa da kuma fatali da kundin tsarin mulkin APC da shugaban ke yi.
Shugabannin jam'iyyar sun kaɗa kuri'ar tsige shi daga mukamin shugaba tare da maye gurbinsa da mataimakinsa a matsayin shugaba na Riko.
Da yake jawabi ga manema labarai, shugaban rikon kwarya, Prince Gilbert C. Chukwunta, yace:
"Mambobin kwamiti sun haɗu domin ceto jam'iyyar mu daga rugujewa matukar Nwoye ya cigaba da jagorancin jam'iyyar APC a jihar."
A wani labarin kuma bayan kwamandojin Boko Haram sun mika makamansu sannan suka nemi yan Najeriya su yafe musu.
Wasu daga cikin yan Najeriya sun nuna fushinsu tare da maida kakkausan radɗi ga tubabbun yan Boko Haram da suka nemi a yafe musu.
Wasu na gani babu dalilin da zaisa a yafe musu kan irin halin tasku da suka jefa al'umma a cikin na tsawon shekaru.
Asali: Legit.ng