Masallatan da Gwamna Zulum ya rusa sun fi cocina yawa – Kungiyar MURIC

Masallatan da Gwamna Zulum ya rusa sun fi cocina yawa – Kungiyar MURIC

  • Kungiyar kare hakkin Musulmi ta MURIC ta yi martani a kan zargin rusa cocina da Gwamna Babagana Zulum yayi a jihar Borno
  • MURIC ta ce sabanin ikirarin da ake yi, masalattan da gwamnatin Borno ta ruguza sun fi cocina yawa
  • Ta ce cocina hudu kacal aka rusa yayin da lamarin ya cika da masallatai 11

Maiduguri, Jihar Borno - Sakamakon takaddamar da ta biyo bayan rushe wasu cibiyoyin ibada a garin Maiduguri, kungiyar kare hakkin Musulmi (MURIC) ta ce sakamakon bincikenta ya nuna cewa a zahiri gwamnatin jihar ta rushe masallatai da cocina ne.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa an yi ta cece -kuce a jihar kan rusau din.

Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Mista Femi Fani-Kayode, shi ma ya bi sahun masu korafin, inda ya zargi gwamnatin jihar da kai hari kan cocina a cikin shirinta na rusau.

Masallatan da Gwamna Zulum ya rusa sun fi cocina yawa – Kungiyar MURIC
Kungiyar MURIC ta ce sakamakon bincikenta ya nuna Zulum ya rusa masallatai 11 da cocina hudu Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Masallatan da aka ruguza sun fi cocina yawa

Kara karanta wannan

Karo na hudu, Abba Kyari ya gurfana gaban kwamitin bincike, an kwashe sa'a 4 yana shan tambayoyi

Amma kungiyar kare hakkin dan adam ta Musulunci, MURIC, ta bayyana cewa hakika gwamnatin jihar Borno ta rushe masallatai 11 da cocina hudu.

Wannan, a cewarta, ya saba da ikirarin cewa cocina kawai aka rushe a jihar.

Daraktan MURIC, Farfesa Ishaq Akintola, ya ce:

“Sabanin farfagandar da aka shirya kan rushe cocin EYN a Maiduguri, kungiyar kare hakkin Musulmai (MURIC) na iya bayar da rahoton cewa tsarin bayanan kasa na jihar Borno (BOGIS) wanda Gwamna Babagana Umara Zulum ya kirkira, ya rushe masallatai 11 da cocina guda hudu, a cikin birnin. An fara atisayen daga ranar 29 ga Mayu, 2019 har zuwa makon da ya gabata.
“Tawagar masu binciken da ke aiki tare da MURIC sun ziyarci kowane rukunin wuraren da aka rusa masallatan, sun yi hira da mazauna garin kuma sun tattara hotuna da bayanan da suka nuna wuraren kowane masallaci daga cikin 11 da ranar da jami’an gwamnatin jihar Borno suka rusa su saboda saba doka.

Kara karanta wannan

Idan laifi Hadiza Bala Usman tayi ya zama wajibi a hukunta ta, Aisha Yesufu

“Bincike ya nuna cewa BOGIS ta rushe masallatai guda biyu a ranar 11 ga Maris, 2020, a kusa da Fato Sandi, a bayan sashen ayyuka a Maiduguri, kusa da fadar Shehun Borno, wanda ke bin Sultan a cikin manyan shugabannin Musulunci a Najeriya. Shehu shine Mataimakin Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA).
“BOGIS ta sake rushe masallatai guda biyu a rana guda (11 ga Maris, 2020), a tsohon ginin Musami da ke kan hanyar Jos a Maiduguri. Haka kuma, an rushe wani masallaci a wannan ranar a wurin da ke kallon NITEL. An rushe wani masallaci a ranar 15 ga Afrilu, 2020 akan titin Kano, kusa da Bulumkutu, Kamfanin Wutar Lantarki na Yola, YEDC. An sake rushe masallatai guda biyu, daya kusa da otal a Galadima wani kuma kusa da bayan Inuwa Timber, a hanyar Baga.
“Masu bincikenmu sun kara gano cewa wasu masallatai guda biyar da aka gani a cikin shataletalen kwastam da ke kusa da hanyar Maiduguri zuwa Bama su ma BOGIS ta rushe su a ranar 23 ga Janairu, 2020, saboda abin da gwamnati ta kira ‘wuce gona da iri.”

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotu ta hana gwamnatin Buhari kame Sunday Igboho

A efe guda, gwamnatin jihar Borno ta bayyana jin daɗinta yayin da ake kara samun karuwar yan ta'adda suna tuba su mika makamansu ga sojoji a jihar.

Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Borno, Alhaji Babakura Abba-Jato, shine ya bayyana haka jim kaɗan bayan kammala taron tsaro a Maiduguri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng