Rushe coci a Maiduguri: An sheke mutum 1 yayin arangama, Zulum ya magantu

Rushe coci a Maiduguri: An sheke mutum 1 yayin arangama, Zulum ya magantu

  • Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya yi alawadai da rikicin rushe wata coci da akayi kuma ya umarci ‘yansanda suyi bincike akai
  • Akalla an kashe mutum daya sakamakon rikicin sannan mutane da dama sun samu raunuka bayan BOGIS sun budewa Jama’a wuta
  • Fustattun matasan, wadanda sakataren BOGIS, Adam Bukar-Bababe ya jagoranta suka rushe cocin EYN ne dake wuraren Maduganari dake cikin babban birnin Maiduguri

Maduganari, Borno - Gwamna Babagana Umara Zulum ya yi Allah wadai da wani rikici wanda yayi sanadiyyar rushe wata coci kuma ya umarci ‘yan sanda su yi bincike akan lamarin.

A kalla mutum daya ne ya rasa ransa yayin da mutane da dama suka samu miyagun raunuka bayan taron ‘yan kungiyar BOGIS sun budewa fararen hula huta yayin da suke rushe wata cocin EYN dake wuraren Maduganari dake babban birnin Maiduguri.

Rushe coci a Maiduguri: An sheke mutum 1 yayin arangama, Zulum ya magantu
Rushe coci a Maiduguri: An sheke mutum 1 yayin arangama, Zulum ya magantu. Hoto daga prnigeria.com
Asali: UGC

PRNigeria sun tattara bayanai akan yadda wasu fusatattun matasa wandanda sakataren BOGIS, Adam Bukar-Bababe ya jagorancesu sannan suka fara rushe cocin ba tare da an yi aune ba.

Kara karanta wannan

Abun bakin ciki: Tsohon sanatan Najeriya ya rasu bayan ‘yar gajeriyar rashin lafiya

Ya rikicin ya fara?

Rikicin ya faru ne bayan wani direba ya afkawa wata coci har yana rusa kujeru, talabinin, firij da sauran abubuwa.

Daga nan ne wani jami’in JTF ya budewa jama’a wuta don a watse daga nan ya kashe wani Ezekiel Bitrus dan shekara 29 sannan ya raunana wasu mutane 5 bayan sun yi kokarin tserewa.

Sakamakon harbin na rashin kula, fusatattun matasa dake gewaye da wurin suka fara zanga-zanga don su nuna takaicinsu akan kashe-kashen da aka yi musu.

Matasa sun yi yunkurin kaiwa sakataren BOGIS hari

Da kyar sakataren BOGIS da samu ya tsere bayan fusatattun matasa sun yi kokarin kai mishi farmaki yayin da sauran ‘yan kungiyarsa suka tsere daga wurin.

Labari ya bayyana yadda wanda yayi harbi ya tsere yayin da sauran jami’an JTF suka cire kayansu suka tsere don gudun a kashesu.

Sannan matasa suka lalata duk wasu ababen hawan jami’an.

Kara karanta wannan

Bakare: Abokin tafiyar Buhari ya ba shi shawarar abin yi, ya daina sukar shugabannin baya

Jami'an tsaro sun kai dauki

Sai da ‘yan sandan jihar Borno suka tura kwamandan Operation Hadin Kai, wadanda kungiyar CAN ta tura don su kawo karshen lamarin.

Sannan gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya umarci ‘yan sandan jihar Borno suyi gaggawar kwantar da tarzomar kuma su yi bincike akan lamarin.

Kakakin gwamnan, Isa Gusau, ya ce gwamnan jihar ya yi wa iyalan wadanda suka rasu ta’aziyya da mika sakon hakurinsa ga wadanda suka raunana.

Gwamnan ya gayyaci shugaban CAN na jihar Borno, Bishop Mohammed Naga kuma ya yi magana dashi akan rikicin da kuma masu cocin EYN na jihar Borno.

Sannan ya umarci mataimakin gwamnan jihar, Umar Kadafur ya kaiwa marasa lafiyar ziyara sannan ya biya duk wasu kudaden da ake bukata.

Bidiyon sojojin Najeriya suna raka yara makaranta a yankin arewa maso gabas

Bidiyon sojoji suna raka wasu daliban makaranta zuwa makaranta a arewa maso gabas a Najeriya ya taba zukatan mutane da dama.

Kara karanta wannan

Miyagu sun kona motoci kurmus, sun kashe Bayin Allah a Jos bayan rikicin da suka barke

Yanzu ‘yan bindiga sun fi harin daliban makaranta don har yanzu akwai sauran dalibai a hannun masu garkuwa da mutane bayan sun sacesu daga makarantunsu.

Sakamakon cigaba da satar dalibai, jihohi da dama suka rufe makarantun sakandare na wani lokaci, shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel