Muna tarairayar 'yan ta'adda: 'Yan Najeriya sun yi martani kan sha tara da arziki da ke baiwa tubabbu

Muna tarairayar 'yan ta'adda: 'Yan Najeriya sun yi martani kan sha tara da arziki da ke baiwa tubabbu

  • Kafar sada zumuntar zamani ta Twitter ta cika da cece-kuce bayan bayyanar wasu hotunan tubabbun Boko Haram
  • A cikin hotuna a nga yadda sojojin Najeriya suke baiwa tubabbun kwamandojin Boko Haram abinci
  • An samu labarin yadda kwamandojin ‘yan Boko Haram suka yi mubaya’a ga sojojin Operation Hadin Kai

Borno - Cece-kuce sun yawaita a kafar sada zumuntar zamani ta Twitter bayan bayyanar hotunan sojoji suna baiwa tubabbun kwamandojin mayakan Boko Haram kayan abinci.

Kwamandojin Boko Haram sun zubar da makamansu sannan sun yi mubaya’a ga sojojin Operation Hadin Kai, The Cable ta wallafa.

A wata takarda ta ranar Litinin, Kakakin sojin, Onyema Nwachukwu, ya wallafa hotunan kwamandojin Boko Haram inda yace Musa Adamu, kwararre akan hada bama-bamai cikin ‘yan Boko Haram yana daya daga cikin wadanda suka tuba.

Muna tarairayar 'yan ta'adda: 'Yan Najeriya sun yi martani kan sha tara da arziki da ke baiwa tubabbu
Muna tarairayar 'yan ta'adda: 'Yan Najeriya sun yi martani kan sha tara da arziki da ke baiwa tubabbu. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Jawabin rundunar soji

Bayan harin kwanannan da rundunar Operation Hadin Kai suka fara bude wa ‘yan Boko Haram na arewa maso gabas wuta babu kakkautawa ya janyo shugaban kwararru a harkar hada bama-bamai, Musa Adamu, wanda aka fi sani da Maka Musa Abuja, da mai binsa a iko, Usman Adamu wato Abu Darda, tare da iyalansa sun mika wuya ga OPHK dake karamar hukumar Bama dake jihar Borno, kamar yadda takardar ta shaida.

Kara karanta wannan

Shugaban mai hada bama-bamai na Boko Haram ya tuba tare da yaransa, ya mika wuya ga sojoji

Sojojin sun baiwa tubabbun ‘yan ta’addan sababbin kayan sawa, kayan abinci da sauran kayan masarufi cikinsu akwai mayaka 335, mata da yara 746 ciki har da matan Chibok.

Tubabbun 'yan Boko Haram sun nemi yafiyar 'yan Najeriya

Tubabbun ‘yan ta’addan sun rike wata takarda wacce a jikinta aka rubuta, “Yan Najeriya ku taimaka kunyafe mana”.

''Yan Najeriya sun yi martani

Kamar yadda The Cable ta ruwaito, tuni 'yan Najeriya suka dinga cece-kuce tare da caccakar gwamnati kan karamcin da take yi wa tubabbun 'yan Boko Haram.

A cewar wani Samuel wanda yayi tsokaci a Twitter:

Za a tankwasa doka ta yafe musu, gwamnati kuma zata girmama su ta hanyar basu kudin jama’a suyi wadaka dasu. Amma matasan Najeriya da suka yi zanga-zanga an mayar dasu tamkar beraye wadanda za a kama a sakaya a gidan yari wasu kuma a kashe. Haka salon mulkin kasar nan yak.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum Ya Bayyana Yadda Yake Farin Ciki da Yan Boko Haram/ISWAP Suke Tuba a Borno

Wani Easy kuwa cewa yayi:

Wannan ai abin takaici ne

Adedayo Adesuyi yace:

Tubabbun ‘yan Boko Haram dauke da rubutun neman gafara. Ya aka yi suka rubuta?

'Yan sanda sun damke babban limamin IPOB da layu tare da harsasai

Rundunar 'yan sanda ta sanar da damke babban limamin masu rajin kafa kasar Biafra, IPOB a jihar Imo, Daily Trust ta ruwaito hakan.

Kamar yadda mai magana da yawun rundunar 'yan sanda na jihar, CSP Mike Abattam ya sanar, wanda ake zargi mai suna Ikechukeu Umaefulem, an kama shi ne a wani wurin bautar gargajiya dake karamar hukumar Ikeduru ta jihar Imo.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan yace an samu bindiga daya da carbi biyar na harsasai tare da abubuwa masu fashewa, tutar Biafra da sauran kayan tsibbu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel