Jirgin NAF yayi luguden wuta a dazukan Niger, 'yan bindiga 70 sun sheka lahira

Jirgin NAF yayi luguden wuta a dazukan Niger, 'yan bindiga 70 sun sheka lahira

  • Ayyukan sojojin sama da na kasa na Operation Gama Aiki (OPGA) suna cigaba da haifar da sakamako mai kyau
  • An samu bayanai akan yadda mazauna yankin jihar Neja suka bayyana yadda aka kashe ‘yan bindiga 70
  • A ranar 5 ga watan Augustan 2021 ne ‘yan bindigan suka sha wannan ragargazar a yankin Jasuwan Garba-Urege

Niger - Ayyukan hadakar sojojin sama dana kasa na Operation Gama Aiki (OPGA) suna kara samar da nasarori na ban mamaki.

PR Nigeria suna cigaba da tattaro bayanai akan yadda ‘yan bindigan dake da sansani a yankin Jasuwan Garba-Urege a jihar Neja sun sha ragargaza a wurin sojojin sama na OPGA da suka yi amfani da Agusta 109 da EC 135 jiragen yaki.

Jirgin NAF yayi luguden wuta a dazukan Niger, 'yan bindiga 70 sun sheka lahira
Jirgin NAF yayi luguden wuta a dazukan Niger, 'yan bindiga 70 sun sheka lahira. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Yadda ragargazar ta kasance

Wani babban jami’in tsaro wanda har da shi aka yi ragargazar ya ce sai da jirgin saman ya bi a sannu wurin gano asalin wuraren da miyagun mutanen suka yi dandazo sannan ya harba abubuwa masu fashewa a wuraren.

Kara karanta wannan

Mutane 10 sun jikkata yayin da sojoji suka dakile wani kazamin rikici a Filato

An hango yadda sansanonin nasu suka yi ta kamawa da wuta sakamakon harbin da suka sha. Rahotonni daga mazauna yankin sun tabbatar da yadda ‘yan bindiga 70 suka bakunci lahira.
Anyi wannan ragargazar ne a ranar 5 ga watan Augustan 2021. Kuma makamancin haka ya kara aukuwa a ranar 6 ga watan Augustan 2021 wanda sojojin sama suka yi a Kwawu da Uzawo dake jihar Neja inda aka ragargaji ‘yan ta’adda da dama.

PDP ga Masari: Ka fito fili ka sanar da Buhari ya gaza, 'yan bindiga sun kwace jiharsa

Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta bukaci gwamna Aminu Masari na jihar Katsina da ya daina jaje kan hauhawar hare-haren 'yan bindiga a jiharsa, TheCable ta wallafa.

A yayin karbar bakuncin Faruk Yahaya, shugaban dakarun sojin kasa wanda ya kai ziyara jihar Katsina a ranar Alhamis, Masari ya ce goma daga cikin kananan hukumomin jihar na fuskantar harin 'yan bindiga a kullum.

Kara karanta wannan

Garkuwa da mutane: Ba a ga daman ceto yaran da ake sace wa bane inji Tsohon Ministan Buhari

A yayin martani ga zancensa, a ranar Lahadi, Kola Ologbondiyan, sakataren yada labarai na jam'iyyar PDP na kasa, yace ya dace Masari ya fito fili ya sanar da shugaban kasa Muhammadu Buhari da jam'iyyar APC cewa gwamnatin tarayya ta gaza.

Asali: Legit.ng

Online view pixel