Za a kashe wanda aka samu da laifin hallaka matarsa, ya birne gawarta a cikin rami

Za a kashe wanda aka samu da laifin hallaka matarsa, ya birne gawarta a cikin rami

  • Kotu ta samu wani magidanci da laifin kashe Mai dakinsa a jihar Jigawa
  • Alkali ya gamsu Rabiu Mamman ya kashe mai dakinsa a shekarar 2016
  • Za a kashe Mamman kamar yadda ya kashe matarsa ta hanyar rataye sa

Jigawa - Babban kotun jihar Jigawa da ke zama a garin Gumel ya zartar da hukuncin kisa a kan wani Rabiu Medin da aka samu da laifin kisan-kai.

Daily Trust ta rahoto cewa an samu Rabiu Mamman mai zama a garin Medin Labo, da ke karamar hukumar Gagarawa, a jihar Jigawa da wannan laifin.

Rahoton ya ce Rabiu Mamman ya aikata laifin kisan-kai, wanda hukuncinsa shi ne a dauki ransa. Amma kotu ba ta iya samun shi da laifin yin karya ba.

A ranar Litinin, 9 ga watan Agusta, 2021, Jaridar ta tabbatar cewa ma’aikatar shari’a ta Jigawa ta fitar da jawabi ta bakin kakakinta, Zainab Baba Santali.

Yadda Mamman ya kashe matar da yake aure

Kara karanta wannan

Abubuwa 20 da na sani game da Limamin Masallacin Quba Sheikh Zarban, Dr Ibrahim Disina

Kamar yadda jawabin ya bayyana, wanda ake tuhuma ya auka wa mai dakinsa a jeji, inda ya rangwala mata itace a kai, wanda ya zama ajalinta.

Bayan ya aikata wannan danyen aiki, sai Rabiu Mamman ya haka rami maras zurfi, ya jefa gawarta.

Babban Kotun Tarayya
Wani babban Kotun Tarayya Hoto: www.heraldnigeria.com
Asali: UGC

“Wajen tabbatar da cewa wanda ake zargi ya aikata laifi, lauyan gwamnati, Jamilu Mohammed ya kira shaidu hudu da suka gabatar da hujjoji a kan wanda ake tuhuma.”
“Shi kuma wanda ake zargi da laifi, ya yi bayani ya na mai kare kan shi, ya musanya zargin da ake yi masa.”

A jawabin na ta, Zainab Baba Santali ta kara da cewa Alkalin da ya saurari shari’ar, ya gamsu cewa an tabbatar da hukuncin kisan-kai a kan Mamman.

A dalilin haka Alkalin kotuya zartar da hukuncin kisan kai ta hanyar rataya kamar yadda sashe na 221 (b) na dokar final kwad ta jihar Jigawa ta yi tanadi.

Kara karanta wannan

‘Yan Sanda sun gurfanar da wani Matashi da ake zargi ya saci N10.7bn a hannun mutane 170

Haka zalika an samu labarin wani Danjuma Haruna da ya kashe matar ‘danuwansa a wani kauye da ake kira Gamatan, a karamar hukumar Miga, duk a Jigawa.

Kakakin ‘yan sanda na Jigawa, ASP Lawan Shiisu Adam, ya shaida wa Daily Post wannan a makon jiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel