Shekara 1 da aure: Hoton dankareriyar motar da mijin Adama Indimi ya gwangwajeta da ita

Shekara 1 da aure: Hoton dankareriyar motar da mijin Adama Indimi ya gwangwajeta da ita

  • Biloniya kuma yariman Kogi, mijin Adama Indimi, Malik Ado-Ibrahim, ya gwangwaje matarsa da kyautar mota a ranar da suke murnar cika shekara daya da aure
  • Masoyan wadanda a ranar Lahadi, 8 ga watan Augusta suka cika shekara daya cif da aure sun tafi wani wuri don cigaba da shagulgulan murna
  • ‘Yar’uwar Adama, Meram, ta wallafa hoton sabuwar motar wacce tayi tsokaci, inda tace “Na shiga so. Ka kasance tare har abada InshaAllah

Hamshakin mai kudin nan, mijin Adama Indimi kuma yariman Kogi, Malik Ado-Ibrahim ya gwangwaje matarsa da kyautar mota a ranar da suka cika shekara daya da aure.

Masoyan wadanda suke shagalin cika shekara daya tare a ranar Lahadi, 8 ga watan Augusta sun tafi wani wuri wanda basu bayyana ba don su cigaba da shagalin.

Shekara 1 da aure: Hoton dankareriyar motar da mijin Adama Indimi ya gwangwajeta da ita
Shekara 1 da aure: Hoton dankareriyar motar da mijin Adama Indimi ya gwangwajeta da ita. Hoto daga @keepingupwiththeindimis
Asali: Instagram

Kanwar Adama, Meram ce ta wallafa hoton kasaitacciyar motar a shafinta na Instagram inda ta rubuta:

Na shiga so. Ku kasance a tare har abada InshaAllah

Kara karanta wannan

Abubuwa 20 da na sani game da Limamin Masallacin Quba Sheikh Zarban, Dr Ibrahim Disina

Hakazalika, shafin 'yan gidansu Adama mai suna @keepingupwiththeindimis ya wallafa a instagram inda suke taya 'yar uwar tasu murnar wannan kyautar girman da aka yi mata.

A shekarar da ta gabata ne aka yi gagarumin shagalin bikin diyar biloniyan Maiduguri da yarima Malik-Ado Ibrahim.

An fara shagalin bikin a Borno kafin daga bisani a koma jihar Kogi inda aka shiryawa amarya Adama gagarumar liyafar cin abincin dare.

PDP ga Masari: Ka fito fili ka sanar da Buhari ya gaza, 'yan bindiga sun kwace jiharsa

Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta bukaci gwamna Aminu Masari na jihar Katsina da ya daina jaje kan hauhawar hare-haren 'yan bindiga a jiharsa, TheCable ta wallafa.

A yayin karbar bakuncin Faruk Yahaya, shugaban dakarun sojin kasa wanda ya kai ziyara jihar Katsina a ranar Alhamis, Masari ya ce goma daga cikin kananan hukumomin jihar na fuskantar harin 'yan bindiga a kullum.

Kara karanta wannan

A karshe IBB ya bayyana yadda aka yi masa lakabi da ‘mugun gwani’ da Maradona

Kamar yadda TheCable ta ruwaito, ya ce rashin tsaron da jihar Katsina ke fuskanta na hana shi bacci.

A yayin martani ga zancensa, a ranar Lahadi, Kola Ologbondiyan, sakataren yada labarai na jam'iyyar PDP na kasa, yace ya dace Masari ya fito fili ya sanar da shugaban kasa Muhammadu Buhari da jam'iyyar APC cewa gwamnatin tarayya ta gaza.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Online view pixel