Ban ki yin biyayya ga umarnin Osinbajo ba, Abubakar Malami

Ban ki yin biyayya ga umarnin Osinbajo ba, Abubakar Malami

  • Ministan shari'a, Abubakar Malami ya musanta rahotanni dake yawo na cewa ya bijirewa umarnin Osinbajo
  • Malami ya sanar da cewa ya bada umarnin yin zabukan jam'iyya ne a matsayinsa na lauya ba antoni janar ba
  • Kamar yadda mai magana da yawunsa ya bayyana, ministan mai bin dokokin kasa ne da na fadar shugaban kasa

FCT, Abuja - Antoni janar na tarayya kuma ministan shari'a, Abubakar Malami SAN, ya musanta rahotanni dake yawo na cewa ya bijirewa umarnin mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo a kan zabukan jam'iyyar APC.

Daga cikin umarnin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Farfesa Osinbajo yayi taron manyan lauyoyi na jam'iyyar a ranar 30 ga watan Yuli domin shawo kan matsalar dake cikin jam'iyyar bayan kotun koli ta yanke hukunci kan zaben gwamnoni na jihar Ondo.

Ban ki yin biyayya ga umarnin Osinbajo ba, Abubakar Malami
Ban ki yin biyayya ga umarnin Osinbajo ba, Abubakar Malami. Hoto daga Channelstv.com
Asali: UGC

An zargi Malami da bijirewa Osinbajo

Akwai rahotanni dake yawo na cewa Osinbjo ya umarci Malami da kada a yi zabukan jam'iyyar na jihohi, Daily Trust ta wallafa.

Kara karanta wannan

IBB ya bayyana mummunan lamarin da zai auku da ba a soke zaben 12 ga watan Yuni ba

Tun farko Malami ya sanar da Daily Trust cewa bai bijirewa umarnin fadar shugaban kasan ba. Ya ce ya bada shawara a yi zabukan ne a matsayinsa na lauya ba na antoni janar na shari'a ba.

A wata takarda da mataimakin Malami na musamman a harkar yada labarai, Umar Gwandu ya saka hannu, AGF yace yadda za a tsara zabukan jam'iyyar abu ne da ya shafi jam'iyyar APC kuma bashi da alaka da na ministan.

Malami ya musanta zargin da aka yi masa

Akwai matukar amfani idan aka bayyana cewa zabuka tare da tarukan jam'iyya duk alhaki ne na jam'iyyar siyasa ba na ofishin antoni janar ba.
Mai girma antoni janar na tarayya da ministan shari'a ba shine ke da alhakin tabbatar da an bi umarnin da ya shafi shugabancin jam'iyya ba kamar yadda aka sani.
A don haka, bai dace da hankali ba idan ake cewa mai girma antoni janar ya ki bin doka wacce bashi da ikon sakawa a shari'ance.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Cike da tashin hankali, Secondus ya koka kan yunkurin 'kwace' PDP

Zargin bai wakilci gaskiyar yadda abubuwa ke tafiya ba. Sanannen abu ne idan aka ce dukkansu biyun lauyoyine, don haka suna da damar bayyana ra'ayinsu kamar yadda sashi na 39 na kundun tsarin mulkin tarayyar Najeriya ya bada na 'yancin sanar da matsaya.
Al'ada ce kuma sanannen abu ne idan aka ce lauyoyi na bayyana matsayarsu kan lamurra wadanda tushensu ba daga kotun koli take ba.
Mai girma Antoni janar na tarayya kuma ministan shari'a zai cigaba da zama mai bin doka tare da kiyaye dukkan umarnin fadar shugaban kasa.

Toshe bakin kafofin yada labarai ba zai yuwu ba, IBB yace

Tsohon shugaban kasan Najeriya na mulkin soji, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya ce duk wani kokarin toshe bakin jama’a ba zai tabbata ba.

Wannan mulkin yayi kokarin tsuke bakin jama’a tuntuni, duk da dai gwamnati ta dade tana musa wannan zargin.

Amma a wata tattaunawa da ARISE TV tayi IBB a gidansa dake hilltop a Minna, jihar Neja a ranar Juma’a, ya ce ‘yan Najeriya ba zasu taba barin hakan ya yuwi ba don zasu jajirce kwarai.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Manyan Shugabannin PDP Na Kasa 7 Sun Yi Murabus

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng