Da dumi-dumi: Najeriya ta yi babban rashi na wani masanin tsaro sakamakon cutar korona
- Kwararre a harkar tsaro a Najeriya kuma mai sharhi a gidan talabijin, Cif Ona Ekhomu, ya mutu
- Marubucin littafin na ‘Boko Haram: Security Considerations and the Rise of an Insurgency’ ya mutu yana da shekaru 66 a duniya
- An tattaro cewa ya mutu ne bayan ya yi fama da cutar korona
Kasar Najeriya a ranar Litinin, 9 ga watan Agusta, ta rasa daya daga cikin fitattun masana harkar tsaro, Cif Ona Ekhomu, wanda ya rubuta littafin, ‘Boko Haram: Security Considerations and the Rise of an Insurgency’.
Jaridar PM News ta ruwaito cewa Ekhomu ya mutu a ranar Litinin, 9 ga watan Agusta, a jihar Legas bayan ya yi fama da cutar COVID-19.
Shugaban na Kungiyar Tsaro da Kariya na Masana'antu na Najeriya (AISSON) ya mutu yana da shekaru 66 a duniya.
An tattaro cewa matar Ekhomu ta tuntubi abokan aikinsa a AISSON kimanin makonni biyu da suka gabata don sanar da su game da rashin lafiyarsa.
Marigayin wanda aka haife a ranar 26 ga Maris 1955 a Irrua, Jihar Edo, Najeriya, ya kasance ƙwararren masanin tsaro a Yammacin Afirka.
Jaridar ta kuma ruwaito cewa marigayin ya yi makarantar sakandare ta Western Boys, Benin City, Jihar Edo kuma ya kammala a 1972.
Bayan haka, ya samu shiga Cibiyar Nazarin Jarida ta Najeriya, Legas, 1974 kafin ya sami digiri a fanninTarihi daga Kwalejin Voorhees, Denmark.
Ya kuma sami digiri na biyu daga Jami'ar Jihar Iowa, Ames, Iowa 1979; da PhD a Harkokin Jama'a da Ƙasashen waje daga Jami'ar Pittsburgh, Amurka 1985.
Ekhomu ya halarci Makarantar Horar da Jami'in Tsaro na Allegheny County a Pennsylvania Amurka a 1986.
Ya sami lasisin Commonwealth na Pennsylvania Dokar 235 Laifin Makamai Masu Mutuka a 1986.
A wani labari na daban, Shugaban rikon kwaryan jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a karamar hukumar Yola ta kudu, Sulaiman Adamu, ya caccaki shugaba Muhammadu Buhari, DailyNigerian ta ruwaito.
Adamu yace da so samu ne, da cutar Korona ta hallaka Buhari mataimakinsa Yemi Osinbajo ya hau kujerarsa.
Asali: Legit.ng