An saki 'dan Yar'adua da ya hallaka mutum hudu da mota a Yola

An saki 'dan Yar'adua da ya hallaka mutum hudu da mota a Yola

  • Bayan kasa da mako guda a kurkuku, an sallami Aminu Yar'adua
  • Kotu ta garkameshi a gidan gyara hali ne kan laifin hallaka mutum da mota
  • Daga cikin wadanda ya hallaka akwai mata 3 ne da namiji 1

Yola, Adamawa - An saki Aminu Yar'adua, dan marigayi Janar Shehu Musa Yar'adua, daga kurkukun Yola bayan sulhu tsakanin iyalan mutanen da ya kashe a hadarin motan da ya auku a jihar.

A ranar Alhamis, kotun majistare da ke zama a garin Yola, jihar Adamawa, ta tsare ‘dan tsohon shugaban Najeriya, Aminu Yar’Adua, a gidan yari.

Hukumar dillacin labarai na kasa, NAN, ta ce Alkali ya bukaci a rike Aminu Yar’Adua mai shekara 36 ne saboda zarginsa da laifin kashe wasu mutane hudu a Yola.

A cewar NAN, dalibin na jami’ar Amurka da ke Najeriya watau AUN, ya jawo wani mummunan hadarin da ya yi sanadiyyar mutuwar wasu Bayin Allah kwanaki.

Kara karanta wannan

GMD ya yi zazzaga a NNPC, an canza wa wasu manyan ma’aikata wuraren aiki, an tsige wani

Ana zargin cewa gangancinsa ne ya kai ga faruwar wannan hadari a ranar Laraba, 23 ga watan Yuni, 2021.

Masu hakkin jini sun ce a biya su diyyar N15m

“Wanda suka mutu a hadarin su ne; Aisha Umar (30), Aisha Mamadu (32), Suleiman Abubakar (2) and Jummai Abubakar (30)."
"Sai kuma Rejoice Annu (28) and Hajara Aliyu (27) da sun samu rauni.”

Jami’in da ya ke karar ‘Yar’adua ya shaida wa kotu cewa ‘yan uwan Aisha Umar, Suleiman Abubakar da Jummai Abubakar suna neman N15m a matsayin diyya.

An saki 'dan Yar'adua da ya hallaka mutum hudu da mota a Yola
An saki 'dan Yar'adua da ya hallaka mutum hudu da mota a Yola
Asali: UGC

An yi sulhu, an sake shi kuma an biya diyya

ThisDay ta tattaro daga gidan gyara hali da kotu cewa an saki Yar'adua bayan sulhu tsakanin iyalansa da iyalan mutum hudu da ya kashe a hadarin.

Wani na kusa da daya daga cikin mamatan, Aisha Umar, wanda ya bukaci a sakaye sunansa yayin hira da manema labarai yace an garzaya da su kotun majistare kuma an bukaci suyi hakuri, su bar lamarin ga Allah.

Kara karanta wannan

Ranar kin dillaci: EFCC ta karbe manyan gidaje, motoci da miliyoyi a hannun wasu ‘Yan damfara 2

Yace:

"An kaimu harabar kotun inda aka ce mu barwa Allah. Kuma tun lokacin muka hakura."

Kan labarin diyya kuwa, yace:

"Ba'a bamu ko sisi ba. Idan an yi wani shiri na kudi toh mu dai bamu sani ba."

Amma wata majiya ta kusa da Aminu Yar'adua ta jaddada cewa an ba iyalan mamatan N15m.

Yace:

"Ina tabbatar muku da cewa an yi sulhu tsakanin iyalan Yar'adua da na mamatan. Abun ya bamu mamaki cewa iyalan Kirista cikin wadanda aka kashe sun ce sun yafe amma na Musulman sun ce sai an biyasu."

"Tuni dai an saki Yar'adua bayan haka kuma ya tafi Katsina don hutu."

Karin bayani kan haka, wani babban jami'in kotun majistare ya bayyana cewa yana da labarin sulhun da akayi amma bai san an bada kudi ba.

Yace:

"Ina da labarin sulhun amma bani da labarin biyyan diyya."

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Online view pixel